Kungiyar RIFAN ta nemi manoma su biya rancen da suka karba

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen Jihar Kaduna ta bayyana damuwarta kan tafiyar hawainiya wajen maido da rancen da ta bai wa ’ya’yanta don bunkasa harkar noma a fadin jihar. Da yake bayyana damuwarsa kan tafiyar hawainiyar da manoman ke yi wajen maido da rancen da uwar kungiyar ta ba su, Shugaban Kwamitin Kula […]

Kungiyar RIFAN ta nemi manoma su biya rancen da suka karba

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen Jihar Kaduna ta bayyana damuwarta kan tafiyar hawainiya wajen maido da rancen da ta bai wa ’ya’yanta don bunkasa harkar noma a fadin jihar.

Da yake bayyana damuwarsa kan tafiyar hawainiyar da manoman ke yi wajen maido da rancen da uwar kungiyar ta ba su, Shugaban Kwamitin Kula da Rarraba Rancen da Maido da shi na Kungiyar RIFAN,  Malam Hassan Tahir, ya gargadi manoman cewa dawo da rancen wajibi ne ba ganin dama ba.

Shugaban wanda ya bayyana haka a garin Gwantu hedkwatar Karamar Hukumar Sanga da ke Jihar Kaduna, ya ce bai kamata wadanda suka ci gajiyar rancen su kure kungiyar har ya zama ba ta da wani zabi, face zuwa kotu don tursasa wa manoman dawo da kudaden ba. Malam Tahir, wanda ya bayyana takaicinsa kan yadda aka karya duk wata yarjejeniya na karbar rancen, ya shawarci manoman da kada su bari lamarin ya kai ga tursasa musu biyan kudaden.

A jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Sanga, Mista Charles Danladi, ya bukaci manoman su rika amfani da rancen da suke karba wajen noma shinkafa mai yawa da inganci da za a rika fita da ita kasashen waje ba na amfanin gida kadai ba.

Ya karfafa wa manoman gwiwa kan karbar rancen tare da shawartarsu su tallata wa sauran manoman batun karbar rancen domin su ma su amfana da shi: “Amma a rika dawo da shi a lokacin da aka yi yarjejeniya,” inji shi.

A karshe Mai martaba Sarkin Fadan Ninzo, Alhaji Umar Musa, ya yi kira ga manoma kan bukatar da ke akwai ta maido wa gwamnati kudadenta a kan lokaci don ci gaba da bunkasa harkar noma a kasar nan.