Kungiyar RIFAN ta yi barazanar yin karar manoman da ba su biya bashi ba
Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen Jihar Kano ta yi barazanar daukar matakin shari’a a kan manoman da suka ki biyan bashin noma da ake kira da “Anchor Borrower” da suka karba a bara. Da yake yi wa manema labarai bayani Shugaban Kungiyar RIFAN ta Jihar Kano Alhaji Abubakar Haruna Aliyu ya ce kungiyar […]
Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen Jihar Kano ta yi barazanar daukar matakin shari’a a kan manoman da suka ki biyan bashin noma da ake kira da “Anchor Borrower” da suka karba a bara.
Da yake yi wa manema labarai bayani Shugaban Kungiyar RIFAN ta Jihar Kano Alhaji Abubakar Haruna Aliyu ya ce kungiyar ta damu sosai game da halin ko-in-kula da wadansu manoma suke nunawa ga shirin na bayar da bashin noma.
Shugaban ya koka kan yadda shirin biyan bashin yake tafiyar hawainiya; inda ya ce mafi yawan manoman da suka ci gajiyar shirin har yanzu ba su dawo da abin da suka karba ba.
Shugaban ya ce duk da cewa akwai bayanan da suke nuna cewa an samu ambaliyar ruwa a yawanicin wuraren da aka yi noma a jihar; haka kuma ya shafi kayan da wadanda suka amfana suka shuka, amma akwai wuraren da aka samu amfani mai kyau.
A cewarsa ko wuraren da ambaliyar ta shafa, manoman sun yi noman rani wanda kuma suka samu amfani mai yawan gaske.
“Don haka muna kira ga mambobinmu su yi kokarin biyan bashin da ke kansu. Kungiya ta dauki wasu matakai wajen karbo bashin. Don haka kungiya a shirye take ta dauki matakin shari’a a kan duk wanda ya ki biyan bashin noman,” inji Shugaban.