Kungiyar Safinatul Khairi ta nemi a rika taimako
Kungiyar Safinatul Kaihri Foundation da ke Kofar Na’isa a Kano ta bukaci al’umma su rika amfani da duk damar da suke da ita wajen taimaka wa junansu ta fuskoki daban-daban. Kungiyar ta yi wannan kira ne lokacin bikin da ta shirya don karrama daya daga cikin ’ya’yanta, tsohon Sakatare ga Babban Mai Taimaka wa Shugaban […]
Kungiyar Safinatul Kaihri Foundation da ke Kofar Na’isa a Kano ta bukaci al’umma su rika amfani da duk damar da suke da ita wajen taimaka wa junansu ta fuskoki daban-daban.
Kungiyar ta yi wannan kira ne lokacin bikin da ta shirya don karrama daya daga cikin ’ya’yanta, tsohon Sakatare ga Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Muradun Karni, Dokta Hassan Sulaiman Kofar Na’isa, a karshen makon jiya.
Kungiyar ta bakin daya daga cikin ’ya’yanta kuma Shugaban Taron, Alhaji Murtala Muhammad ta ce an karrama Dokta Hassan ne bisa gudummawar da ya bayar wajen ci gaban yankin da Jihar Kano baki daya.
Da yake bayyana abubuwan ci gaba da Dokta Hassan ya gudanar a yankin, Alhaji Murtala ya ce dubban mutane a yankin sun samu aiki a wurare da dama a matakin Tarayya da ta jiha ta hanyar Dokta Sulaiman. “Zan iya cewa Allah ne kadai Ya san iyakacin mutanen da Dokata Hassan ya sama wa aiki a wannan yanki. A yanzu haka a cikin wadanda ya sama wa aiki akwai wanda har ya kai matsayin Darakta a gwamnatin jiha. Har a yanzu kuma yana yin wannan aiki sai dai idan bai ga wata dama ba,” inji shi.
Ya kara da cewa baya ga ayyukan taimakon al’umma da Dokta Hassan ya ce, “A yanzu kuma ga wani abin alheri da ya samar na gina mana asibiti tare da samar da dukkan kayayyakin da asibitin ke bukata da ba al’ummar yankin ne kadai za su amfana da shi ba har da al’ummar Jihar Kano baki daya.”
Ya yi kira ga jama’a su taimaki junansu da dan abin da suke da shi ba sai sun kai wani matsayi babba ba. “Ita harkar taimako ba sai mutum ya mallaki wani abin duniya mai yawa ko ya taka wani babban matsayi ba, domin wanda ake karramawa a yau ya fara taimako tun yana hidimar kasa, inda a wancan lokacin ya sama wa wani aiki. Haka ya ci gaba da taimaka wa mutane a duk matakan da ya rike a jiha da tarayya har zuwa lokacin da ya iyi ritaya, wata biyu da suka gabata,” inji shi.
Da yake jawabi wanda aka karramar Dokta Hassan Sulaiman ya gode wa kungiyar bisa karramawar da ta yi masa; inda ya yi alkawarin ci gaba da bayar da gudunmawa wajen bunkasa yankin da Jihar Kano.
Ya yi kira ga masu rike da madafun iko da su yi amfani da damarsu saboda mulki ba abu ne tabbatacce ba. “Ina kira ga duk wanda yake da wani mukami ya yi amfani da damarsa wajen bunkasa yankin da ya fito da taimaka wa al’ummarsa. Idan mutum bai yi haka ba, to, zai yi nadama daga baya wanda ba zai yi masa amfani ba,” inji shi.