kungiyar Seleka ta kori membobinta da ke cikin gwamnatin hadaka

kungiyar Musulmi ta Seleka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kori membobinta da suka shiga sabuwar gwamnatin hadaka, inda ta ce ba su tuntube ta ba kafin su yi hakan.Mataimakin Shugaban kungiyar Nouredine Adam  ne ya bayyana hakan, inda kuma ya kara da cewa, “ ba mu mika sunan kowa ba dangane da mukamin firaminista, […]

kungiyar Seleka ta kori membobinta da ke cikin gwamnatin hadaka
kungiyar Seleka ta kori membobinta da ke cikin gwamnatin hadaka

kungiyar Musulmi ta Seleka a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta kori membobinta da suka shiga sabuwar gwamnatin hadaka, inda ta ce ba su tuntube ta ba kafin su yi hakan.
Mataimakin Shugaban kungiyar Nouredine Adam  ne ya bayyana hakan, inda kuma ya kara da cewa, “ ba mu mika sunan kowa ba dangane da mukamin firaminista, ko ministoci  . Saboda haka ne duk wani dan kungiyarmu da ya karbi wani mukami a wannan sabuwar gwamnatin, ba da yawunmu ya yi ba. Kuma mun ja layi tsakanin mu da shi. ”
Masana dai na cewa  wannan matakin ya kara jefa shakku akan korewar sabuwar gwamnatin kasar kuma wani koma-baya ne a kokarin da ake na kawo karshen rikicin siyasar kasar.  Rikicin da ke barazanar raba kasar gida biyu, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma tilasta wa wasu da dama kauracewa gidajensu.
Har ila yau, ba kungiyar Seleka ba ce kawai ta samu wannan barakar. kungiyar  Kwato ’Yancin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, karkashin jagorancin tsohon firaminista Martin Ziguele, ita ma tana fuskantar irin wannan matsalar,  inda a ranar Litinin ta bayyana cewa ta sallami duk wani membanta da ya karbi mukami a sabuwar gwamnatin.
kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ta fada rikici ne tun bayan da Mista Michel Djotodia ya jagoranci kungiyar Seleka ta kai farmaki babban birnin kasar, Bangui, inda ya karbe mulki a watan  Maris din shekarar 2013.