kungiyar Sha’iran Najeriya ta bayyana sakamakon gasar waka

kungiyar Sha’iran Najeriya reshen Jihar Kano (PIN Kano), ta fitar da sakamakon gasar da ta shirya kwanakin baya, domin tunawa da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da kuma taya sarki na yanzu, Muhammadu Sanusi II murnar cika shekara uku bisa karaga. A wata takarda da kungiyar ta raba wa manema labarai, ta bayyana cewa: […]

kungiyar Sha’iran Najeriya ta bayyana sakamakon gasar waka

kungiyar Sha’iran Najeriya reshen Jihar Kano (PIN Kano), ta fitar da sakamakon gasar da ta shirya kwanakin baya, domin tunawa da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da kuma taya sarki na yanzu, Muhammadu Sanusi II murnar cika shekara uku bisa karaga.

A wata takarda da kungiyar ta raba wa manema labarai, ta bayyana cewa: “Muna farin cikin sanar da duk wadanda suka samu damar shiga gasar rubutun wakokin da aka shirya a cikin watan Yuli, 2017 don tunawa da gudunmawar Marigayi Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da kuma taya mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II murnar cika shekara uku a karaga, cewa alkalan gasar cikin harsunan Hausa da Turanci, wadanda suka hada da Malam Nasiru G. Ahmad, Malam Sulaiman S. Maibazazzagiya, Malama Bilkisu Yusuf Ali, Ismail Bala, Dokta Saka Aliyu da Maryam Alhamdu sun kammala aikinsu cikin nasara. Kuma har sun fitar da sunayen zakarun da ake sa ran za su yi nasarar lashe mataki na daya zuwa na uku a gasar guda biyu.”

Takardar ta ci gaba da cewa: “Daga cikin wadannan zakakuran mawaka guda bakwai a kowane bangare. Ga bayanin sunan wakar da mawakin da garin kowannensu kamar haka: Zakarun gasar cikin harshen Hausa, (a)Taurarin Kano Biyu daga Abdulhamid Muhammad Sani Matazu (Malumman Matazu) Katsina. (b) Jallabar Hausa daga Abu Warakat Ayagi Kano. (c) Kamar Kumbo Kamar Kayanta daga Hafiz Koza Adamu Katsina. (d) Kano Me Abin Koyi daga Ibrahim Hamisu Kano. (e) Tabbas Ita Ke Jawo Baki daga Isah Aliyu Abdulrahman Sakkwato. (f) Kano Mai Sarautar Asali daga Rukayya Muhammad Bello Kebbi. (g) Abjadiyya daga Shamsu Hamza Kaduna.

“Zakarun gasar cikin harshen Turanci kuwa sun hada da (a) ‘From Transformation’ daga Amara Femoh Sesay Goron Dutse, Kano. (b) ‘Long Libe The King’ daga Bappa Maryam Idris Zaria, Kaduna. (c) ‘Prince of Kano’ daga Hassan Mohammed Usman Minna, Niger. (d) ‘A Tribute to Late Alhaji Dr. Ado Bayero’ daga Mariya Abdullah Sidi Daurawa, Kano. (e) ‘Song of Bayero’ daga Mustapha Ibrahim Abdullahi Zango, Kano. (f) ‘Home City’ daga Safiyya Kabir Rijiyar Zaki, Kano. (g) ‘Mai Tagwayen Masu’ daga Sani Ammani Nomansland, Kano.”

Jami’ar hulda da jama’a ta kungiyar, Maryam Gatawa ta bayyana cewa za a gabatar da bikin raba kyaututtuka ga wadanda suka samu nasara, a yayin wani taro na musamman da kungiyar PIN za ta shirya a cikin watan Nuwamba na bana, a Kano. Kamar yadda ta ce: “Taron za a gabatar da shi ne domin yabawa da kuma gode wa dukkan wadanda suka samu damar aiko da wakokinsu domin shiga wannan muhimmiyar gasa. Muna kuma jinjina wa alkalan da suka yi wannan alkalanci.”