kungiyar Tambarin Arewa ta samar da asusun tallafa wa yara
Wata kungiya mai suna Tambarin Arewa ta ’yan Arewa da ke zaune a Legas ta samar da asusu na musamman domin tallafa wa yaran da ke zaune a cikin jihar ta Legas, saboda ganin yadda wasu iyaye ba su da karfi agaza wa ’ya’yansu domin samun ilmi nagartacce.kungiyar ta ce sau tari akan samu yara […]
Wata kungiya mai suna Tambarin Arewa ta ’yan Arewa da ke zaune a Legas ta samar da asusu na musamman domin tallafa wa yaran da ke zaune a cikin jihar ta Legas, saboda ganin yadda wasu iyaye ba su da karfi agaza wa ’ya’yansu domin samun ilmi nagartacce.
kungiyar ta ce sau tari akan samu yara hazikai, amma rashin wanda zai tallafa musu su yi karatu, sai ka ga sun fada wata rayuwar da ba ta dace ba, don haka daga yanzu duk wani yaro haziki da ta samu labarinsa kuma ba ya da wanda zai agaza masa, za ta dauki nauyinsa.
Sakataren kungiyar Barista Isah Buhari ya ce ta haka ne za su ba da gudunmowarsu ga matasa, kuma haka zai iya kauda su daga gararamba, musamman ganin yadda rayuwa take a birnin Ikko, wadda ta sha bamban da ta Arewa. ya ce muddin ana ci gaba da nuna halin ko-oho ga harkar ilimi, to ba shakka al’umma ba za ta ci gaba ba.
Dangane da inda kungiyar za ta rika samun kudin da za ta yi wannan taimako, sai ya ce daga harajin da za su rika yi wa su kansu ’ya’yanta da kuma neman tallafi daga kamfanoni masu zaman kansu sai kuma bude wajen ajiya, wanda za su rika amfana da shi a bisa tsarin ajiya, kwatankwacin na banki.
Shi ma shugaban kungiyar, Alhaji Mustafa Ibrahim ya ce baya ga taimaka wa yara, kungiyar za ta agaza wa masu sana’ar hannu, kuma za ta rika wayar musu da kai a kan batun wuraren da gwamnatin jihar ta hana a yi kasuwanci, lamarin da jahiltarsa ke sa su shiga tsaka-mai-wuya a hannun jami’an tsaro.
Daga karshe kungiyar ta ja kunnen ’yan Arewan su kasance masu bin doka da oda, wanda ta haka ne zamansu zai ci gaba, ya yi tasiri.