kungiyar Telolin Gyara Kayanmu ta nemi taimako don koyar da matasa sana’a
kungiyar telolin Gyara Kayanmu da ke Bauchi ta nemi gwamnati ta agaza musu da kayan aiki, kamar yadda ta alkawarta don su ci gaba da koyar da matasa sana’o’i don a rage zaman garari tsakaninsu.Shugaban kungiyar, Mista Fransis Ramat shi ne ya bayyana haka a yayin da wakilinmu ya ziyarci ofishinsa don ganin yadda suke […]
kungiyar telolin Gyara Kayanmu da ke Bauchi ta nemi gwamnati ta agaza musu da kayan aiki, kamar yadda ta alkawarta don su ci gaba da koyar da matasa sana’o’i don a rage zaman garari tsakaninsu.
Shugaban kungiyar, Mista Fransis Ramat shi ne ya bayyana haka a yayin da wakilinmu ya ziyarci ofishinsa don ganin yadda suke gudanar da ayyukan koya wa matasa sana’ar dinki da sauran sana’o’in hannu. Ya nemi taimakon masu hali da gwamnati su himmatu don bude wuraren da za a rika taimaka wa matasa su dogara da kansu.
Mista Fransis ya ce Gwamna Malam Isa Yuguda ya zauna da su, ya bayyana murnarsa kan yadda telolin suke koyar da matasa ayyukan dogaro da kai, kuma ya yi alkawarin tallafa wa kungiyar da kayan aiki, amma har yau sakon bai isa gare su ba. “Kuma hakan ba ta hana mu aiki da aljihunmu ba wajen horas da matasan sana’a kyauta, a matsayin tamu gudummowar ga al’umma. Tun bai zama gwamna ba, ya taimaka wajen bude inda ake koyar da sana’ar tela, don haka muke ba shi uzuri game da rashin cika alkawarin. Agaza wa kungiyoyi yana rage wa gwamnati wahalolin lura da mutanenta”. Inji shi.
Shi ma uban kungiyar, Alhaji Ali Gambo Tela ya shawarci dukkan telolin da ke fadin Jihar Bauchi su rike kungiyar da muhimmanci, su ci gaba da koya wa matasan sana’a, ba tare da sun karbi komai ba, saboda ba su dogaro da gwamnati suna gudanar da ayyukansu bisa kashin kai kuma kyauta.
Abdullahi Musa Naira yana cikin telolin da suke koyar da matasa a kungiyar, ya bukaci teloli su rike sana’arsu da muhimmanci don samun cigaba, musamman ta fuskar kowa ya nuna hikimarsa wajen koyar da matasan dinki da saka da rini da aikin wuyan riga.
Hannatu Dauda, shugabar mata a kungiyar, ta koka game da yadda matasa ke shiga halin shaye-shaye da fada da juna, don haka ta kirayi mata su tashi tsaye kan tarbiyyar yaransu. “Muna horas da matasa yadda za su shiryu su zauna da juna lafiya ta hanyar dogaro da kai da kuma yadda za su yi zaman arziki a cikin al’ummarsu.