kungiyar wasan Polo ta Katsina ta zabi sababbin shugabanni
kungiyar wasan kwallon Dawaki watau Katsina Polo Club ta zabi shugabannin da za su ci gaba da jagorancin kungiyar. Shugabanta na dindindin wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ya ce,”wa’adi ne ya yi na sake zaben shugabannin da za su cigaba da jagorancin kungiyar, saboda haka ina kira ga masu zabe da su natsu su […]
kungiyar wasan kwallon Dawaki watau Katsina Polo Club ta zabi shugabannin da za su ci gaba da jagorancin kungiyar. Shugabanta na dindindin wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna ya ce,”wa’adi ne ya yi na sake zaben shugabannin da za su cigaba da jagorancin kungiyar, saboda haka ina kira ga masu zabe da su natsu su zabi wadanda suke ganin za su jagorance su bisa adalci, kasancewar duk wanda aka gani a nan ba an ba shi kudi ba ne ya zo, ko ya zo ne don ya samu kudi, a’a, ra’ayi ne tare da son wasan ya kawo shi tare da ganin cewa wasan ya cigaba kamar yadda aka sani cewa Katsina ita ce cibiyar wasan kwallon Polo a kasar nan tun zamanin Marigayi Sarkin Katsina Dikko wanda shi ne ya kawo wasan daga Ingila”.
Baya ga zaman ‘yan kungiyar a dunkule a kan rabu gida biyu a duk lokacin da batun zabe ya zo, wato zaben da ‘yan wasa ne kadai za su zabi wanda zai jagorance su. Zaben Kyaftin da mataimakinsa ne ‘yan wasa ke yi ba tare da tsoma bakin sauran membobi ba . Sauran mukamai kuwa dukkan ‘yan kungiyar ke gabatar da shi.
Zaben da akayi a ranar Lahadin makon da ya gabata, baya ga shugaba na din-din-din wato Alhaji Lawal Kaita an kuma zabi Alhaji Abdu Usman (Majidadin Katsina) a matsayin shugaba kuma Manajan shirya wasan na Polo, sai Alhaji Salisu Ado Shinkafi (Bunun Katsina) mataimaki na daya sai Alhaji Sabo Usman (danmadamin Katsina) mataimaki na biyu. Alhaji Abdu Maska Sakataren kungiyar yayin da Malam Umar Kabir ya zamo Kyaftin tare da Alhaji Madani Sani a matsayin mataimakin Kyaftin.
Sauran sun hada da Alhaji Sani Lawal BK Sakataren kudi da Alhaji Hamza Sule Maiyawo Mai bincike sai Kabir Ahmed S/kuka Jami’in hulda da jama’a watau (PRO) tare da Nasiru Wali mataimakin PRO.
Sannan an zabi ranar 5 ga watan Satumbar wannan shekara a matsayin ranar da za a fara gasar kwallon Polo a Katsina wanda kuma shi ne mabudin gasar ta wannan shekara ga sauran garuruwan da ake yin sa a duk fadin kasar nan.