Kungiyar WBFA ta ilimantar da mata kan renon ciki
kungiyar Samar da Lafiya a Afirka (Wellbeing Foundation Africa) ta wayar da kan matan da ke sansanin ’yan gudun hijira na unguwar Wassa a Birnin Tarayya Abuja kan yadda ake renon ciki da haihuwa. Tawagar kungiyar wacce ta hada da babbar jami’ar tsare-tsare ta Abuja, Dokta Yewande Ayoola da jami’ar tsare-tsare ta kungiyar reshen Jihar […]
kungiyar Samar da Lafiya a Afirka (Wellbeing Foundation Africa) ta wayar da kan matan da ke sansanin ’yan gudun hijira na unguwar Wassa a Birnin Tarayya Abuja kan yadda ake renon ciki da haihuwa.
Tawagar kungiyar wacce ta hada da babbar jami’ar tsare-tsare ta Abuja, Dokta Yewande Ayoola da jami’ar tsare-tsare ta kungiyar reshen Jihar Legas, Misis Eunice Akhigbe da hadin gwiwar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) da ke Abuja sun ziyarci sansanin ’yan gudun hijirar ne don ilimantar da matan da ke sansanin yadda ake renon ciki har zuwa haihuwa.
Matan wadanda mafi yawancinsu suna dauke da juna biyu sun bayyana cewa wannan ne karo na farko da wata kungiya ta taba ilimantar da su kan yadda ake renon ciki da haihuwa.
kungiyar bayan ta kammala ilimantar da su sai ta raba musu sabulai da man shafawa da wasu sinadarai na yi wa jarirai da wanka.
Shugaban sansanin Mista Hamman Abubakar ya bayyana ziyarar da kungiyar ta kai a matsayin wani ci gaba domin a cewarsa sai matan sun yi tafiya ta rabin sa’a sannan za su samu asibiti.
Shugabar kungiyar WBFA, Misis Toyin Saraki ta bayyana takaici kan yadda ake samun karuwar kalubalen kiwon lafiya a sansanin ’yan gudun hijira a duniya saboda karuwar masu gudun hijira daga sassan duniya.
“Muna bukatar zaman lafiya domin yaran da aka haifa a cikin yaki su samu kwanciyar hankali. Kafin nan dole sai mun dauki matakan da suka kamata wajen kare lafiyar yara da mata wadanda yaki ya raba da gidajensu. Ta wannan kokari ne za mu samu ceton da muke bukata,” inji ta.
Babbar jami’ar tsare-tsare ta Abuja ta kungiyar WBFA, Dokta Yewande Ayoola ta ce kungiyar ta tsara shirin ne don ta kai dauki ga mata masu juna biyu tare da ilimantar da su hanyoyin rainon ciki.
Dokta Ayoola ta ce darussan da matan suka koya za su taimaka musu wajen dauke musu fargabar ciki da haihuwa da goyo da kuma shayarwa.
Matan da suka samu horo a sansanin ’yan gudun hijirar sun bayyana gamsuwarsu dangane da dauki tare da taimakon da kungiyar ta kawo musu.