Kungiyar Yakin Zaben Buhari za ta kafa kwamiti a dukan kananan hukumomin Najeriya
Ganin yadda aka dage takunkumin yakin neman zaben badi, Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta Buhari Campain Organisation (BCO) ta ce za ta kafa kwamitin wayar da kan jama’a kan irin ayyukan da Shugaban Kasa ya yi a kananan hukumomin Najeriya da dukan runfunar jefa kuri’a na kasar nan. Shugaban Kungiyar Alhaji […]
Alhaji Danladi Garba Pasali
Ganin yadda aka dage takunkumin yakin neman zaben badi, Kungiyar Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ta Buhari Campain Organisation (BCO) ta ce za ta kafa kwamitin wayar da kan jama’a kan irin ayyukan da Shugaban Kasa ya yi a kananan hukumomin Najeriya da dukan runfunar jefa kuri’a na kasar nan.
Shugaban Kungiyar Alhaji Danladi Garba Pasali ne ya bayyana haka, lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos, inda ya ce za su kafa kwamitoci a dukan kananan hukumomin kasar nan 774, da kowace rumfar zabe da ke Najeriya, don wayar da kan jama’ar Najeriya kan irin ayyukan da Shugaban Kasa Buhari ya yi a Najeriya, a kusan shekara 4 da ya yi kan kujerar shugabanci.
Ya ce Shugaba Buhari ya yi fada da ’yan ta’adda, inda ya kawo zaman lafiya a kasar nan. Kuma ya juya akalar ’yan Najeriya zuwa ga harkokin noma. Y yi aikin hanyoyin da aka manta da su a baya. Ya farfado da hanyoyin jiragen kasa. Ya kama wadanda suka sace kudaden kasar nan tare da kwato kudaden. Kuma ya taimaka wa masu kananan sana’o’i da tsofaffi.
Don haka ya ce za su kafa wadannan kwamitoci, don su wayar da kan jama’a, kan wadannan ayyuka da Shugaba Buhari ya yi.
Alhaji Danladi Pasali ya yi bayanin cewa ’yan Najeriya ba za su taba mantawa da irin illar da Jam’iyyar PDP ta yi ba.
Sannan ya yi kira ga talakawan Najeriya su kara daura damara wajen jawo hankalin ’yan uwansu wajen ganin Shugaba Buhari ya sake komawa kujerar shugabancin kasar nan, domin ya ci gaba daga inda ya tsaya.