kungiyar ’yan acaba ta yaba da bude Cibiyar Inganci ta Bauchi
kungiyar ’Yan Acaba ta Jihar Bauchi ta yaba bude Cibiyar Inganci da fitaccen dan kasuwa Alhaji Balali Muli ya yi don samar wa matasa aikin yi. Shugaban kungiyar Alhaji Sani Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin da ake bikin bude Cibiyar Inganci a Bauchi a ranar Litinin.Ya ce: “Dole a gode wa Alhaji Balali […]
kungiyar ’Yan Acaba ta Jihar Bauchi ta yaba bude Cibiyar Inganci da fitaccen dan kasuwa Alhaji Balali Muli ya yi don samar wa matasa aikin yi.
Shugaban kungiyar Alhaji Sani Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin da ake bikin bude Cibiyar Inganci a Bauchi a ranar Litinin.
Ya ce: “Dole a gode wa Alhaji Balali saboda gudunmuwar da yake bayarwa wajen taimakon matasa.”
Ya bukaci matasan da za su yi aiki a cibiyar su kasance masu gaskiya da rikon amana, su sani duk abin da suka yi za a tambaye su.
Alhaji Balali Shugaban Cibiyar Inganci ya ce matasa suna daga cikin wadanda suke ba da gudunmawa wajen bunkasa harkokin yau da kullum, don haka zai ci gaba da tallafa musu har su tsaya da kafafunsu.
Ya ce, “Na bude cibiyar ne domin ganin na ba da tawa gudunmawa wajen samar wa matasa hanyoyin dogaro da kai. Zan ci gaba da tallafa wa matasa don su tsaya da kafafunsu, wanda hakan ne zai sa su taimaka wa wadansu, don haka nake kira al’umma su rika tallafa wa matasa don a magance sace-sace da sara-suka. ”
Barista Jibrin S Jibrin wani lauya ne ya jagoranci bude cibiyar, ya ce tabbas samar wa matasa aikin yi zai magance matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya.
An raba lita uku-uku na mai ga ’yan Acaba 200 da suka halarci wajen bude cibiyar.
Da yawa daga cikin ’yan Acabar da Wakilinmu ya zanta da su sun bayyana godiyarsu ga Cibiyar Inganci da ke taimaka wa matasa.
Wani dan acaba mai suna Khalid Hassan ya ce yanzu sun fahimci illolin da ke tattare da zaman kashe wando a tsakanin matasa.