Kungiyar ‘yan Arewa a Legas sun goyi bayan Buhari da Sanwo-Olu

Kungiyar ’yan Arewa magoya bayan APC a Jihar Legas sun fara kamfe na zaben Shugaba Buhari a karo na biyu da kuma dan takarar Gwamnan Jihar Legas a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Babajide Sanwo-Olu. ’Ya’yan kungiyar sun bayyana haka ne a wurin taron rantsar da Alhaji Zakari Muhammed wanda aka fi sani da ‘Zaki’ a […]

Kungiyar ‘yan Arewa a Legas sun goyi bayan Buhari da Sanwo-Olu
Kungiyar ‘yan Arewa a Legas sun goyi bayan Buhari da Sanwo-Olu

Kungiyar ’yan Arewa magoya bayan APC a Jihar Legas sun fara kamfe na zaben Shugaba Buhari a karo na biyu da kuma dan takarar Gwamnan Jihar Legas a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Babajide Sanwo-Olu.

’Ya’yan kungiyar sun bayyana haka ne a wurin taron rantsar da Alhaji Zakari Muhammed wanda aka fi sani da ‘Zaki’ a matsayin Shugaban Kungiyar na Karamar Hukumar Eti Osa.

A kokarin kungiyar na jaddada goyon bayanta, inji sabon shugaban, sun sasanta bambance-bambancen da ke tsakanin ’ya’yan kungiyar a lungu da sako na Karamar Hukumar Eti Osa da kuma Ikoyi-Obalende.

Zaki ya ce “Na zo Legas daga Adamawa a 1983 kuma na shiga siyasa a 1999. Ni mai biyayya ne ga jam’iyya kuma Asiwaju Bola Tinubu shi ne ubanmu a siyasance, duk abin da ya umarce mu shi za mu yi. Saboda haka ne muka fara yakin neman kuri’a ga Shugaba Buhari da kuma Babajide Sanwo-Olu.”

Ya ci gaba da cewa, “Mun fahimci cewa ba za mu cimma nasara ba har sai mun dinke baraka a tsakanimmu kuma wannan shi ne abin da muka cimma a karkashin shugabancina a Karamar Hukumar Eti Osa. Mataki na gaba shi ne mu fara yin kamfe a aikace ga Shugaban Kasa da Gwamna da kuma sauran ’yan takara a karkashin  APC.”

Shugaban Kungiyar ’Yan Arewa magoya bayan APC ta Jihar Legas, Alhaji Muhammad Dandama ya ce, samuwar shugaban kungiyar a matakin karamar hukumar zai saukaka musu harkokin kamfe, kuma zai taimaka musu wurin samar wa jam’iyya kuri’u masu yawa saboda yawan al’ummar ’yan Arewa a yankin.