kungiyar ’Yan Arewa a Ogun ta bude kasuwarta
kungiyar Hadin kan Mutanen Arewa ta bude kasuwar da wani Basaraken Yarabawa ya ba ta a karamar Hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun.Kasuwar da aka bude a ranar Lahadin da ta gabata za a rika sayar da kayayyaki da dabbobi, kuma za a gina mayanka nan gaba.Basaraken da ya ba kungiyar kyautar kasuwar mai suna Olasodi […]
kungiyar Hadin kan Mutanen Arewa ta bude kasuwar da wani Basaraken Yarabawa ya ba ta a karamar Hukumar Ewekoro ta Jihar Ogun.
Kasuwar da aka bude a ranar Lahadin da ta gabata za a rika sayar da kayayyaki da dabbobi, kuma za a gina mayanka nan gaba.
Basaraken da ya ba kungiyar kyautar kasuwar mai suna Olasodi Olalekan, Baale na Akomo, ya shaida wa Aminiya cewa ya yi haka ne domin ya kara dankon zumuncin da ke tsakaninsa da ’yan Arewa.
“A Jihar Bauchi na yi hidimar kasa bayan na kammala karatuna a jami’ar garin. Sun yi mini halacci kuma na taso na ga iyayena tare da jama’ar Arewa na rayuwa ta zaman lafiya da sanin mutumcin juna a Sabo, Abeokuta.,” inji Basaraken, wanda ya yi fatan ’yan Arewar za su ci gaba da nuna dattako irin nasu, su kuma yi zaman lafiya tsakaninsu da mutanen garin Ewekoro da ma duk wadanda za su zo a ci kasuwar da su. Ya kuma ja hankalin mutanen garin Ewekoro da su bai wa mutanen Arewar hadin kai, su kuma mutunta su a inda ya ba su tabbacin cewa da sannu za su samu tagomashin ci gaban da kasuwar za ta kawo wa yankin da ma jihar baki daya.
An dai bude taron da karatun Alkur’ani Mai girma daga bisani aka yi yanke-yanken dabbobi da aka yi walima da su. daruruwan manyan ’yan kasuwa ne suka halarci taron tare da sarakunan gargajiya.
A jawaban da shugabanin kungiyar suka gabatar, sun yi kira ga duk wani dan kasuwa mai sha’awar yin kasuwanci a kasuwar cewa kofa a bude take kuma a yanzu ba za a rika karbar kudin haraji ba bare na jangali. Fatansu kawai shi ne duk mai sha’awa, a ko’ina yake ya zo a raya kasuwar da shi.