kungiyar ’Yan Arewa mazauna Amurka ta nemi a rika ba mata fifiko wajen neman ilimi

kungiyar ’yan asalin Arewacin Najeriya da ke zaune a Amurka ta koka a kan yadda ake fifita maza fiye da mata a wajen neman ilimin boko a matakin firamare da kuma na sakandare musamman a Arewacin Najeriya.kungiyar wacce ake kira Arewa Progressibe Forum-USA (APF-USA) ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar mai […]

kungiyar ’Yan Arewa mazauna Amurka ta nemi a rika ba mata fifiko wajen neman ilimi
kungiyar ’Yan Arewa mazauna Amurka ta nemi a rika ba mata fifiko wajen neman ilimi

kungiyar ’yan asalin Arewacin Najeriya da ke zaune a Amurka ta koka a kan yadda ake fifita maza fiye da mata a wajen neman ilimin boko a matakin firamare da kuma na sakandare musamman a Arewacin Najeriya.
kungiyar wacce ake kira Arewa Progressibe Forum-USA (APF-USA) ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sanya hannun shugabanta Umar Muhammad da kuma sakatarenta Martins Ocholi.  kungiyar ta ce ganin cewa a ranar 11 ga watan Oktoba mai zuwa ne za a yi bikin ranar ’yan mata ta duniya ya sa ta yi wannan kira ga gwamnatocin da ke sassan duniya musamman na Najeriya a kan a rika kula da ilimin mata kanana kamar yadda ake kula da na bangaren maza.
kungiyar ta ce fiye da rabin duniya ba su cimma nasara wajen daidaita sha’anin karatun maza da na mata ba musamman a matakin firamare da kuma na sakandare.
kungiyar ta ce abin bakin ciki ne ganin cewa babu wata kasa daga Nahiyar Afirka da kuma Kudu da Sahara da ta shiga jerin kasashen da suke kula da ilimin mata kamar yadda ya dace kamar yadda rahoton da Asusun Kula da Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNESCO) ya fitar ba.
kungiyar ta ce a binciken da ta yi, ta gano daga shekarar 2000 kawo yau, ya nuna kasashen da suka samu nasara wajen ba da damar neman ilmi daidai-wa-daida a tsakanin jinsin maza da jinsin mata a matakin firamare da kuma sakandare bai wuce kashi 36 daga cikin 100 ba.  kungiyar ta ce hakan ta sa ake tauye hakkin mata kanana su kimanin miliyan 52 daga samun ilimi a matakin firamare zuwa na sakandare.
kungiyar ta ce ganin yadda a arewacin Nijeriya ne aka fi samun ‘yan matan da ake tauyewa hakkinsu na neman ilmi, da kuma yadda suke cikin tsananin talauci, ta sa kungiyar tsara jadawalin yin kamfe a Najeriya ta yadda kasar za ta kai ga shiga jerin kasashen da suka samu nasara wajen ba jinsin maza da mata damar neman ilimi daidai-wa-daida.
kungiyar ta ce a binciken da ta yi ta gano daga cikin kowane yara 10 da ke shiga makanatar firamare a Arewacin Najeriya,  8 daga ciki maza ne yayin da biyu kacal ne mata.  Sai dai kungiyar ta ce an dan samu cigaba a matakin sakandare inda daga cikin kowane dalibi 10 ake samun mace hudu ko biyar da ke yin karatu.  Amma duk da haka abin ya ragu a matakin karatun jami’a inda ake samun maza sun nunka mata wajen yin karatu.
Daga nan kungiyar ta bayar da shawarar hanyoyin da suka kamata a bi wajen ganin an ba mata damar yin karatu daidai da maza.  Daga cikin shawarwarin akwai bayar da ilimi kyauta ga mata, da kuma bullo da tsarin da zai bai wa ’yan matan da ba su yi makarantar firamare ba damar yin haka da kuma karfafa musu gwiwar cigaba da yin karatu har matakin sakandare.   Sannan a rika horar da malaman da ke koyar da su da kuma samar musu ingantattun kayayyaki ga malaman da kuma daliban da sauran bukatu na yau da kullum.
kungiyar APF-USA dai kungiyar ce mai zaman kanta.  kungiya ce da ta dukufa wajen tabbatar an bunkasa sha’anin ilimi musamman ga mata a matakin firamare da kuma sakandare a Arewacun Najeriya.  kungiyar taka bayar da tallafi sannan kuma tana bayar da tallafi ga irin wadannan yara mata da suke karatu musamman ma a Arewacin Najeriya.