kungiyar ’yan canji ta Arik ta yi sabon shugaba
kungiyar ’yan canji rashen Arik da ke daura da filin saukar jirgin sama na cikin gida da ke Legas, ta zabi sabon shugabanta, Alhaji danladi Idris Ahmad, wanda aka fi sani da danladi Sunday.Sabon shugaban dai yayi nasarar doke abokin takararsa, Alhaji Yakubu Mahmuda Kamfala a zaben da kungiyar ta gabatar a harabar rukunin rumfunan […]
kungiyar ’yan canji rashen Arik da ke daura da filin saukar jirgin sama na cikin gida da ke Legas, ta zabi sabon shugabanta, Alhaji danladi Idris Ahmad, wanda aka fi sani da danladi Sunday.
Sabon shugaban dai yayi nasarar doke abokin takararsa, Alhaji Yakubu Mahmuda Kamfala a zaben da kungiyar ta gabatar a harabar rukunin rumfunan ’yan canjin da ke Arik a Legas.
Sabon Shugaban ya sha alwashin damawa da dukkanin ’yan kasuwar, domin ganin sun cin ma muradunsu na ci gaban kasuwar. Saboda a cewarsa, ya shaida salon mulkin tsoffin shugabbanin kungiyar tun daga lokacin Alhaji Muhammadu Mai Gwanjo. Ya kuma yaba wa abokin takararsa, Alhaji Yakubu Mahmuda Kamfala bisa dattakunsa da cikar kamala, wanda ya ce mutum ne masani mai son gaskiya da rikon amana. Ya kuma shawarce shi da kada ya karaya, ganin ya fito takara sau biyu yana shan kayi, domin a cewarsa Shugaba Buhari sau uku yana shan kayi sai ga shi yanzu Allah Ya ba shi.
A nasa jawabin, Alhaji Yakubu Kamfala taya abokin takararsa murna ya yi domin a cewarsa nasarar tasu ce gaba daya. Kana ya kara da cewa daya daga cikin alkawarin da ya yi wa ’yan kasuwar na dauke wa tsofaffi da suran marasa karfi kudin da ake biya duk sati a kasuwar, duk da cewa bai ci zabe ba, zai biya musu kudin har na tsawon wata uku. Ya kuma sha alwashin baiwa sabon shugaban kungiyar hadin kai don ganin an ciyar da kasuwar gaba. Tsohon shugaban riko na kungiyar, Alhaji Garban Jabbo, yabawa ya yi da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Kana ya yi fatan alheri ga sabon shugaban kungiyar dama daukacin ’yan kasuwar canjin da ke Arik.