Kungiyar ‘yan daba sun harbi matashi a rumfar zabe ta Ibadan
Wani matashi mai suna Monsuru ya gamu da ajalinsa a dalilin harbin bindiga da Kungiyar ‘yan dabar siyasa mai suna “One Million Boys” ta yi a lokacin da jama’a suke kada kuri’a a jiya Asabar a rumfar zabe ta Ward 2 dake Kudeti a Ibadan. Al’amarin ya auku ne da misalin karfe 2 na rana […]
Wani matashi mai suna Monsuru ya gamu da ajalinsa a dalilin harbin bindiga da Kungiyar ‘yan dabar siyasa mai suna “One Million Boys” ta yi a lokacin da jama’a suke kada kuri’a a jiya Asabar a rumfar zabe ta Ward 2 dake Kudeti a Ibadan.
Al’amarin ya auku ne da misalin karfe 2 na rana a lokacin da magoya bayan Jam’iyar Zenith Labour suka fara cire hotunan ‘yan takarar wasu jam’iyyu daga jikin banguna suna maye gurbinsu da na su hotunan. A daidai wannan lokaci ne ‘yan wannan kungiya ta ‘One Million Boys’ suka fara harbin bindiga domin tarwatsa taron jama’a. Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta tabbatar da aukuwar lamarin da tace ta fara binciken gano masu hannun haddasa rikicin.