kungiyar ’Yan Jarida ta bukavi a kawo karshen kashe – kashe a Zamfara
Shugaban kungiyar ’yan jarida ta kasa rashen Jihar Zamfara ya nemi gwamnatin jihar da ta kawo karshen yawan kashe-kashen jama’a da satar shanu da garkuwa da mutane da yake kara ta’azara a jihar.Alhaji Mainasara dan Sarki ya nemi gwamnatin tarayya da ta karawa jihar jami’an tsaro da kayan aiki don kawo karshen al’amarin, kamar yadda […]
Shugaban kungiyar ’yan jarida ta kasa rashen Jihar Zamfara ya nemi gwamnatin jihar da ta kawo karshen yawan kashe-kashen jama’a da satar shanu da garkuwa da mutane da yake kara ta’azara a jihar.
Alhaji Mainasara dan Sarki ya nemi gwamnatin tarayya da ta karawa jihar jami’an tsaro da kayan aiki don kawo karshen al’amarin, kamar yadda ya bayyana a wata takarda da ke daule da sa hannun Sakataren kungiyar Alhaji Abubakar Ahmed, wadda aka raba wa manema labarai a garin Gusau.
Shugaban ya ve kiran ya zama wajibi ne ganin yadda ake kashe mutane mazauna kauyuka wadanda ba su jiba ba su gani ba.
kungiyar ta bayyana bakin vikinta na ganin irin mawuyavin halin da mazauna kauyukan da abin ya shafa suke vikin kan irin wannan hare-hare da ake yawan kai masu. Daga nan kungiyar ta bukavi gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar da shugabannin kananan hukumomi da su hada hannu su samar da wata hanya kwakkwara da za ta kawo karshen al’amarin a jihar, don fidda wadanda abin ya shafa daga vikin mawuyavin halin da suka tsinvi kansu a viki.
Har ila yau, Hukumar Agajin Gaggawa NEMA a Jihar Zamfara ta yi kira da babban murya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya duba yiwuwar samar da karin tallafi da aka ba su.