kungiyar ’yan jarida ta koka kan karancin ilmantar da maniyyata
kungiyar ’yan jarida da ke sa ido a kan hakkokin mahajjata (Independent Hajj Reporters ( I.H.R) ta koka a kan karancin ilmantar da maniyyata aikin hajji daga bangaren hukumar alhazai. Shugaban kungiyar Malam Muhammad Ibrahim ne ya bayyana a makon jiya yayin wata ziyara da kungiyar ta kai a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda […]
kungiyar ’yan jarida da ke sa ido a kan hakkokin mahajjata (Independent Hajj Reporters ( I.H.R) ta koka a kan karancin ilmantar da maniyyata aikin hajji daga bangaren hukumar alhazai.
Shugaban kungiyar Malam Muhammad Ibrahim ne ya bayyana a makon jiya yayin wata ziyara da kungiyar ta kai a hedikwatar hukumar da ke Abuja, inda ya bayyana aniyar kungiyar na shiya horo ga jami’an hukumar da ke gudanar da bangaren ilmantar da jama’a da watsa labarai da ke jihohi.
kungiyar wadda ta yaba da ci gaban da aka samu a cikin kankanen lokaci a karkashin jagorancin shugaban hukumar alhazai ta kasa Alhaji Muhammad Musa Bello a bangaren safara, samar da masauki da kuma kula da lafiyar maniyyata, ta bukaci karin azama a bangaren ilmantarwan.
kungiyar ta ce ilimantar da maniyyata zai magance matsalar kura-kurai da mahajjatan Najeriya ke tafkawa a yayin aikin hajji a kasa mai tsarki.
Shugaban hukumar alhazai ta kasa Alhaji Muhammad Musa Bello ya bayyana godiyarsa a kan ziyarar, sannan ya bukaci kungiyar ta bada sunan mutum biyu daga bangarenta wadanda za su zauna da jami’ai uku daga bangaren hukumar don tsara yadda za a bada horon a nan gaba.