Kungiyar ‘yan Keke Napep ta tallafa wa ’ya’yanta

Kungiyar masu haya da Keke Napep da aka fi sani da ‘Ƙurkura ko a Daidaita Sahu’ dake Jihar Katsina sun rabawa ’a an ƙungiyar sabbin Ƙurƙuraye biyu don tallafa masu su dogara da kansu, maimakon zaman jiran tsammani. A makon da ya gabata ne aka yi bikin hannunta wa su ’a an wannan ƙungiya waɗanda […]

Kungiyar ‘yan Keke Napep ta tallafa wa ’ya’yanta
Kungiyar ‘yan Keke Napep ta tallafa wa ’ya’yanta

Kungiyar masu haya da Keke Napep da aka fi sani da ‘Ƙurkura ko a Daidaita Sahu’ dake Jihar Katsina sun rabawa ’a an ƙungiyar sabbin Ƙurƙuraye biyu don tallafa masu su dogara da kansu, maimakon zaman jiran tsammani. A makon da ya gabata ne aka yi bikin hannunta wa su ’a an wannan ƙungiya waɗanda Allah Ya ba sa’a suka sami wannan tallafi na waɗannan a Daidaita Sahu guda biyu. Kamar yadda Shugaban ita wannan Ƙungiya na Jiha Malam Jamilu Isyaku ya bayyanar.

Yace ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne domin ganin cewa ’a an ƙungiyar suna amfana daga irin an kudaɗen da ƙungiyar ke samu daga hannunsu kuma take tarawa har Allah Ya basu ikon ɓullo da wannan shiri na sayawa membobin marasa ƙurƙurar domin ganin cewa sun samu kuma suna aiki da su domin dogaro da kansu kuma su ciyar da iyalansu.

Shugaban ya ƙara da cewa,wannan shiri shine na farko da ƙungiyar ta ɓullo da shi wanda kuma zai cigaba. “Mun tattara kudaɗen ne daga resitin ƙungiya da ake sayarwa duk mako, tare da sauran hanyoyin da ƙungiyar ke bi tana samun kuɗin shiga. To sai muka ga ya dace mu sayo Ƙurƙurar mu ba waɗanda ba su samu waɗanda suka ba su ba, domin kasan mafi yawansu na jama’a ne suke saye suna bayarwa ana yi masu haya. To wasu za ka taras kodai wadda suke da ita ta lalace ba a gyara ba ko kuma wani dalili ya sanya mai ita ya karɓa. To shine maimakon mutum yayi ta zama haka nan, shine muka ɓullo da wannan hanya. Kuma ana yin zaɓe ne ga wanda Allah Ya ba. Malam Jamilu ya ƙara da cewa, shirin yana da nufin ganin cewa, waɗanda suka samu wannan tallafi sun yi ƙoƙarin biya cikin lokacin da akayi yarjejeniya domin su mallake su baki ɗaya. Kamar yadda yace, an sayi kowane Keke Napep akan Naira dubu 660. Ya ƙara da cewa, irin wannan hanyar ce kaɗai ƙungiya zata amfanar da membobinta. “Zamu cigaba da sayar da wannan resiti da kuma yin rajistar don cigaba da kawo wasu shirye-shiryen. Kuma wannan duk daga aljihun ƙungiya ne ba tare da samun tallafi daga ko ina ba. Kazalika, muna roƙon sauran membobi da su cigaba da yin biyayya da kuma kiyaye dokokin ƙungiyar. Sannan ita kuma gwamnati muna roƙo da ta riƙa tallafawa Ƙungiyoyin masu sana’a irin tamu domin rage zaman kashe wando a tsakanin al’umma.

Wadanda suka amfanar, sun nuna farin cikinsu tare da tabbatar da cewa za su kiyaye duk wasu dokokin da aka gindaya masu. Sun jinjinawa shugabannin wannan ƙungiya akan wannan namijin ƙoƙari.