Kungiyar ’Yan Lemo ta bukaci gwamnatin Nasarawa ta tallafa mata

Kungiyar ’Yan Lemo ta Babban Kasuwar Lemo ta garin Maraba da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa ta bukaci yi gwamnatoci a matakin karamar hukuma da jiha da masu hannu da shuni da sauran cibiyoyin da suka dace su rika tallafa wa mambobinsu da jari don ba su damar bunkasa kasuwancinsu. Shugaban Kungiyar Alhaji […]

Kungiyar ’Yan Lemo ta bukaci gwamnatin Nasarawa ta tallafa mata

Alhaji Hussaini Jibrin Abdullahi shugaban kungiyar ‘yan lemo a Maraba

Kungiyar ’Yan Lemo ta Babban Kasuwar Lemo ta garin Maraba da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa ta bukaci yi gwamnatoci a matakin karamar hukuma da jiha da masu hannu da shuni da sauran cibiyoyin da suka dace su rika tallafa wa mambobinsu da jari don ba su damar bunkasa kasuwancinsu.

Shugaban Kungiyar Alhaji Husaini Jibrin Abdullahi ne ya yi wannan kira lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa.

Ya ce ba shakka rashin isasshen jari ne babban kalubale da ’ya’yan kungiyar a kasuwar suke fuskanta; inda ya yi kira ga gwamnatoci da sauran hukumomin da suka dace su rika tallafa musu da jari ko bashi don bunkasa kasuwancinsu.

Ya ce ’ya’yan kungiyar suna bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban jihar da kasa baki daya ta hanyar kasuwancinsu na saya da sayar da lemo da kankana da gwanda da abarba da sauransu.

Shugaban ya ce mutane na zuwa daga ciki da wajen jihar don yin kasuwanci da su. Saboda haka ya kamata gwamnatoci da sauran masu ruwa-da-tsaki baki su rika kai ziyartar kasuwar don gane wa idanunsu harkokin kasuwanci da ke gudana tare da tallafa musu da jari.

Shugaban ya bayyana wasu daga cikin nasarori da kungiyar ta samu a kasuwar cikin shekara daya da wata uku na shugabancinsa; wadanda ya ce sun hada da gina babban ofishin kungiyar da yake da kananan ofisoshi shida da babban dakin taro daya; wanda  ake saran kammala aikin kafin karshen bana. Ya ce akwai kuma tsara albashin ma’aikatan kasuwar da ke rike da mukamai daban-daban, wanda shi ne karon farko da aka tsara irinsa a tarihin kasuwar da biyan masu aikin tsaron kasuwar da kama musu ofishi da sauransu.

Dangane da kalubale da kungiyar ke fuskanta a yanzu, Alhaji Hussaini Abdullahi, ya ce bayan matsalar rashin isasshen jari sauran matsaloli da kungiyar ke fuskanta a yanzu da suke jawo cikas ga harkokinta sun hada da karancin kudaden shiga da ke zuwa asusun kungiyar, kuma bukatu sun yi wa kungiyar yawa da sauransu.

A karshe ya bukaci mambobin kungiyar da sauran ’yan kasuwar, su ci gaba da bai wa shugabanninsu cikakken goyon baya, tare da yin hakuri sakamakon yadda ya ce ake samun ci gaba da canje-canje a hankali.