Kungiyar ’yan Midilbelt ta caccaki TY Danjuma kan kalamansa

  Kungiyar da ke rajin kare muradun al’ummar tsakiyar Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da kungiyoyin kasa da kasa su dora alhakin duk wata tarzoma da ta auku a yankin a kan tsohon ministan tsaro TY Danjuma.   Kungiyar ta yi kiran ne yayin da take mayar da martani ga kalaman da TY Danjuma ya […]

Kungiyar ’yan Midilbelt ta caccaki TY Danjuma kan kalamansa

 
Kungiyar da ke rajin kare muradun al’ummar tsakiyar Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da kungiyoyin kasa da kasa su dora alhakin duk wata tarzoma da ta auku a yankin a kan tsohon ministan tsaro TY Danjuma.
 
Kungiyar ta yi kiran ne yayin da take mayar da martani ga kalaman da TY Danjuma ya yi na yin kira ga jama’a su kare kansu inda ta ce kiran da tsohon ministan ya yi zai kara rura wutar rikici a yankin.
 
Shugaban kungiyar na kasa, Yarima Raymond Enero ya ce kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen maka tsohon ministan a kotu muddin rikici ya tashi a yankin.
 
Ya bukaci TY Danjuma ya janye kalaman da ya yi cikin gaggawa tare da canja kiran da ya yi ga jama’a na amincewa da kokarin da gwamnati take yi na maganin kalubalen da ke fuskantar yankin na fadan fulani da manoma.