kungiyar ’yan sintiri za ta taimaka a gudanar da zaben 2015

Mataimakin kwamandan kungiyar ’yan sintiri ta Najeriya na jihohin Arewa ta Tsakiya Alhaji Garba Juji ya bayyana cewa kungiyarsu ta shirya don taimaka wa gwamnati da sauran al’ummar Najeriya don a gudanar da zabubbukan shekarar 2015 lafiya.  Alhaji Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos a makon […]

kungiyar ’yan sintiri za ta taimaka a gudanar da zaben 2015
kungiyar ’yan sintiri za ta taimaka a gudanar da zaben 2015

Mataimakin kwamandan kungiyar ’yan sintiri ta Najeriya na jihohin Arewa ta Tsakiya Alhaji Garba Juji ya bayyana cewa kungiyarsu ta shirya don taimaka wa gwamnati da sauran al’ummar Najeriya don a gudanar da zabubbukan shekarar 2015 lafiya. 

Alhaji Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos a makon jiya.
Ya ce babu shakka idan aka sanya ’yan sintiri a cikin gudanar da zabubbukan masu zuwa, to za a yi lafiya a tashi lafiya.
“Mu ’yan sintiri kanmu a hade yake, muna cikin al’umma ne babu ruwanmu da maganar kabilancin ko kuma addini. A cikinmu akwai kowace irin kabila da ke kasar nan, kuma akwai mabiya kowane addini a kasar nan.” Inji shi.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su sanya ’yan sintiri a cikin jami’an tsaron da za su lura da harkokin zaben da za a gudanar, “yin hakan zai sa mu bada gudunmuwar don tabbatar da zabe mai inganci.”
“Ina kira ga dukkan ’yan kungiyar sintiri ta Najeriya su rike wannan aiki bisa amana da kishin kasa.” Ya ce daga karshe.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya