kungiyar ’yan walda ta gyara tebura da kujerun wasu makarantu kyauta a Jihar Katsina
kungiyar masu sana’ar walda da cigaban matasa ta Jihar Katsina ta gudanar da gyaran tebura da kujerun da suka lalace a makarantun sakadare mallakar gwamnati kyauta a jihar, a karon farko na bayar da gudunmawarsu kan ilimi. Shugaban kungiyar, Alhaji Abbati Abdulkareem ya shaida wa manema labarai cewa sun dauki wannan mataki ne na bayar […]
kungiyar masu sana’ar walda da cigaban matasa ta Jihar Katsina ta gudanar da gyaran tebura da kujerun da suka lalace a makarantun sakadare mallakar gwamnati kyauta a jihar, a karon farko na bayar da gudunmawarsu kan ilimi.
Shugaban kungiyar, Alhaji Abbati Abdulkareem ya shaida wa manema labarai cewa sun dauki wannan mataki ne na bayar da tasu gudunmuwar don tallafa wa gwamnati a kan ciyar da ilmi gaba a fadin jihar. “kokarin gwamnati a wajen cigaban ilimi a fadin jihar, ya sa muka ga ya zama wajibi gare mu iyaye, mu bayar da duk wata gudunmuwarmu a wannan fanni. Shi ya sa mu, a kungiyance, muka yanke shawarar yin amfanin da abin da Allah Ya ba mu na tallafa wa wannan kuduri. Mun kasa jihar shiyya uku, wato yankin Daura da Funtuwa da kuma Katsina, a matakin farko”. Inji shi.
Shugaban ya ce a kowace shiyya sun dauki wasu makarantu da yawan adadin kujeru da teburan da suka gyara. A shiyyar Daura akwai makarantar sakandare ta jeka-ka-dawo ta ’yanmata da ke Daura, inda aka gyara 100; sai kuma wata sakandaren jeka-ka-dawo guda 100; a Karkarku guda 100; sai ta Kalgo.
“A shiyyar Funtuwa ma akwai Kolejin gwamnati inda muka gyara 190 a garin Funtuwa;100 a Faskari da Kabomo da Bakori da dandume, mai 110.
“A shiyyar Katsina akwai Kwalejin gwamnati, 300; sai sakandaren gwamnati ta jeka-ka-dawo da ke kofar ’Yandaka, 400; da kuma makarantar koyon addinin ta tunawa da sarkin Katsina, Sir Usman Nagogo, wadda aka fi sani da suna ATC, 300; dukkansu a cikin garin Katsina”. Inji shi.
Don samun saukin gudanar da ayyukan, kungiyar ta rarraba su ga ‘ya’yanta da ke zaune a shiyyoyin, bayan kafa wasu ‘yan kananan kwamitoci da suka kula da wasu sassa na gudanar da ayyukan. Akwai kwamiti mai kula da kayan aiki a karkashin kulawar Alhaji Junaidu; sai mai kula da halartar ma’aikata, a karkashin Alhaji Yusuf Abbas; sai kwamitin tantance aiki karkashin Alhaji Abdulkadir Rafindadi da kuma kwamitin bayar da agajin farko ko da an samu wata matsalar rashin lafiya, a karkashin kulawar shugaban kungiyar na jiaha.
Da yawa membobin kungiyar sun samu halartar ayyukan tare da kayan aikinsu, wadanda suka hada da injinan bayar da hasken wuta, wadanda kusan ma da su ne ake gudanar da ayyukan, sannan kuma an samu gudunmuwar kayan aiki daga wadanda ba su samu damar halartar aikin ba.
Alhaji Abbati ya kalubalanci duk wata kungiyar da ke kiran kanta kungiya da ta fito ta rika ba da tata gudunmuwar ta kowace fuska don cigaban yanki da al’umma da jiha da ma kasa baki daya. Sannan ya yi kira ga jama’a da su rika tallafa wa wasu ayyukan da gwamnatoci ke gudanarwa, “Ba zura ido ga komai a yi mana ba”, inji shi.
A nasa jawabin, a madadin sauran shugabannin makarantun da suka amfana da gudunmuwar kungiyar, shugaban makarantar sakandaren jeka-ka-dawo ta Kofar ‘Yandaka, Alhaji Lado Barau ya nuna jin dadinsu ga irin wannan aiki da ya kira irinsa na farko daga wata kungiya mai gudanar da sana’o’in hannu masu zaman kansu, kuma a matsayin kyauta, ba tare da an biya su ko sisi ba. A kan haka shugaban makarantar ya ja hankalin jama’a da su yi koyi da kungiyar, wadda ta tallafa wa harkar ilmi, wanda yake ginshikin cigaban kowa a duniya.
Alhaji Lado ya ankarar da iyaye kan batun kula da ilimin ‘ya’yansu ta hanyar bayar da gudunmuwarsu ko da kuwa ta ziyarar makarantun ne don ganin halin da yaransu, tare da ita makarantar ke ciki.