kungiyar ’yan walda ta yi gyaran kujeru kyauta a Katsina
A kwanakin baya ne Shugaban kungiyar Masu Sana’ar Walda na Jihar Katsina Alhaji Sani Ado Kwa ya ce kungiyarsu ta gudanar da gyaran kujeru da tebura a makaratun gwamnati domin bayar da gudunmuwarta na tallafawa harkokin ilmi a fadin jihar. Shugaban ya ce, “irin yunkurin da Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ya yi na sake […]
A kwanakin baya ne Shugaban kungiyar Masu Sana’ar Walda na Jihar Katsina Alhaji Sani Ado Kwa ya ce kungiyarsu ta gudanar da gyaran kujeru da tebura a makaratun gwamnati domin bayar da gudunmuwarta na tallafawa harkokin ilmi a fadin jihar.
Shugaban ya ce, “irin yunkurin da Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari ya yi na sake farfado da martabar ilimi a jihar ya sa kungiyar ta bi sahu don bayar da gudunmuwar ta. Muna da yakinin irin matakin da gwamnan ya dauka na inganta ilimi za a samu nasara fiye da yadda ake tunani. Saboda wannan kungiyarmu ta ga ya dace ta bayar da gudunmuwarta don taimaka wa wannan yunkurin gwamnati. Mun rarraba wannan aiki na gyaran kujeru da tebura kashin farko ya zuwa yankuna uku,inda muka dauki makarantun jeka ka dawo uku-uku daga kowace shiyya.”
A shiyyar Katsina mun dauki karamar hukumar Charanci,Batsari da Dutsin-ma. Sai shiyyar Funtuwa, inda muka dauki karamar hukumar kankara da Faskari da dandume. Sai kananan hukumomin Daura, Mai’aduwa da Zango daga shiyyar Daura.
Shugaban ya kara da cewa,kowace shiyya sun yi aikin da za a kiyasta kudinsu akalla naira milyan biyu-biyu.
Kodayake, wannan shi ne zagayen farko na aikin, har ila yau, kungiyar ta ba da tabbacin cewa nan gaba kadan za a fara zagaye na biyu.