kungiyar YCEEF za ta yi taron addu’a ga Shugaba Buhari

Wata kungiyar kare ’yancin dan Adam da wayar da kan matasa tare da koya musu sana’a da ake kira da Youth for Change Enlightenment and Empowerment Foundation (YCEEF), za ta gudanar da taron addu’ar neman Allah Ya bayar da lafiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Shugaban kungiyar ta kasa, Malam Aminu Ibrahim dantinau ne ya […]

kungiyar YCEEF za ta yi taron addu’a ga Shugaba Buhari

Wata kungiyar kare ’yancin dan Adam da wayar da kan matasa tare da koya musu sana’a da ake kira da Youth for Change Enlightenment and Empowerment Foundation (YCEEF), za ta gudanar da taron addu’ar neman Allah Ya bayar da lafiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar ta kasa, Malam Aminu Ibrahim dantinau ne ya bayyana haka yayin da ya kawo zirayar musamman ga ofishin Aminiya da ke Abuja a shekaranjiya Laraba.

Malam Aminu dantinau ya ce sun shirya taron addu’ar ne don nuna wa duniya cewa Shugaba Buhari yana da muhimmanci ga al’ummar Najeriya.

Shugaban ya ce za su gudanar da taron ne ranar 15 ga Agustan bana a Dandalin Eagle Skuare da ke Abuja.

Ya cewa bayan gudanar da taron na kasa mabiya addinin Musulunci da Kirista za su gudanar da addu’a ta musamman a wuraren ibadunsu a ranakun Juma’a da Asabar da kuma Lahadi. Ya ce kungiyar ita kadai ta dauki dawainiyar shirya taron tare da tabbatar da samun nasararsa.

dantinau ya ce sun kafa kungiyar ce kimanin shekara 15 da suka gabata don wayar da kan matasa da koya musu sana’o’i domin dogaro da kansu. Ya ce kungiyar ta samu nasarori masu yawa wadanda suka hada da koya wa matasa sana’o’i a wurare da dama tare da tallafa musu da jari.

Sai dai ya ce kungiyar tana fuskantar matsaloli masu yawa da suka hada da rashin samun tallafi daga masu rike da madafun iko don tallafa wa matasan da suka koyi sana’o’in.

dantinau ya ce sana’o’in da kungiyar take koya wa matasa sun hada da sana’ar fenti da kanikanci da facin taya da sauran sana’o’i masu yawa. Ya ce burin da kungiyar take son cimmawa shi ne a samu matasa wadanda suka waye tare da koyon sana’a don dogaro da kansu. Hakan kamar yadda ya ce ita ce hanyar da za samu ingattacciyar al’umma mai dogaro da kanta.