Kungiyar Zakirai ta karrama Sarkin Bauchi
kungiyar Zakirai (Hilakuz Zikri) ta kasa reshen Jihar Bauchi ta karrama Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu da lambar yabo ta kasa. Da yake mika masa lambar yabon da Alkur’ani Mai girma da kuma carbi a fadarsa, fitaccen malamin Musuluncin nan kuma jagorar darikar Tijjaniyya, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya gode wa Sarkin […]

kungiyar Zakirai (Hilakuz Zikri) ta kasa reshen Jihar Bauchi ta karrama Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu da lambar yabo ta kasa.
Da yake mika masa lambar yabon da Alkur’ani Mai girma da kuma carbi a fadarsa, fitaccen malamin Musuluncin nan kuma jagorar darikar Tijjaniyya, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya gode wa Sarkin Bauchi kan kokarin da yake yi wajen samar da zaman lafiya a masarautarsa da jihar baki daya.
Sheikh dahiru Bauhci ya kuma bayyana addu’a a matsayin ita ce kawai babbar hanya da za a bi domin magance bala’o’in da ke addabar kasar nan, kamar satar mutane don garkuwa da su a karbi kudin fansa da satar shanu da fashi da makami da yaki da Boko Haram da kuma fadace-fadacen Fulani makiyaya da manoma.
Malamin wanda dansa Sayyadi Bashir Sheikh dahiru ya wakilce shi ya nanata muhimmancin zama lafiya da kwanciyar hankali wajen samun ci gaban kasa. Ya ce kafin zakirai su kawo wannan ziyarar sun bi wajensa kuma ga carbi na hannunsa da ya ce su hada wa Mai martaba Sarki da shi da kuma Alkur’ani Izu Sittin tunda gidansu gidan Alkur’ani ne da zikirin Allah.
Ya ce idan mutum yana cewa walittaka ba gaskiya ba ce, ta gidajen sarautu da Shehu Usmanu ya kafa su ne suke nuna karfin karamar walittaka domin dauloli da dama sun rushe gwamnatoci da dama sun tafi zamaninsu ya kare, amma wadannan gidajen sarautu suna nan daram tunda waliyyi ne ya kafa su kuma kowane mai mulki ya zo sai ya girmama su, ya kara zamanantar da su domin su ci gaba da tafiya da zamanin har illa masha Allahu.
Tun da farko Shugaban kungiyar ta Jihar Bauchi, Alaramma Abdullahi Shu’aibu ya ce “Mun zo fada ne don karrama Sarkinmu kuma jagoranmu a matsayinsa na Uban kungiyar Zakirai ta Jihar Bauchi, kuma dan Tijjaniyya wanda muke yin zikiri tare kuma wanda ba abin da ya fi so a duniya kamar zikiri da karatun Alkur’ani kuma duk lokacin da aka tambaye shi abin da yake fada ke nan, ko lokacin da aka ba shi sarauta da aka tambaye shi cewa me ya fi so, ya ce zikiri da karatun Alkur’ani kowa ya ji da kunnensa a rediyo.”
Sannan sai ya gode wa Sarkin saboda adalcin da yake nunawa wajen jagorancin al’ummar jihar, sannan ya roke shi da kada ya yi kasa a gwiwa wajen tsayawa a kan hidimar addini wanda shi ne abin da ya kafa gidansu.
Ya kuma yaba wa Sarkin saboda irin goyon baya da karfafa gwiwa da yake yi wa Zakirai a kowane lokaci, sannan ya roki Allah Madaukakin Sarki Ya yi masa sakayya.
A jawabin Mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu ya gode wa Zakiran saboda karrama shi da suka yi kuma ya ce ya sadaukar da lambar girmamawar da suka ba shi ga babansa Sheikh dahiru Usman Bauchi.
Sarkin ya hori al’umma da su kula da istigfari da hailala kuma su zauna lafiya da juna kuma ayi zumunci da aikata ayyukan alheri da kuma taimakon juna.
A lokacin ziyarar, an yi ta rera zikiri tare da yin addu’oin na musamman domin samun zama lafiya da kwanciyar hankali da karuwar arziki a jiha da kuma kasa baki daya.