kungiyar Zamzamiyya ta sami sabon shugaba
kungiyar Taimakon Musulunci mai sunan Zamzamiyya ta gudanar da zabe, inda Alhaji danladi Zage ya zama sabon shugabanta.kungiyar ta gudanar da zaben ne a unguwar Agumalu da ke cikin yankin Apapa da ke Jihar Legas, inda ’yan takara uku suka fafata neman kujerar shugaba, inda Alhaji danladi Zage ya zo na daya; Alhaji dan Asabe […]
kungiyar Taimakon Musulunci mai sunan Zamzamiyya ta gudanar da zabe, inda Alhaji danladi Zage ya zama sabon shugabanta.
kungiyar ta gudanar da zaben ne a unguwar Agumalu da ke cikin yankin Apapa da ke Jihar Legas, inda ’yan takara uku suka fafata neman kujerar shugaba, inda Alhaji danladi Zage ya zo na daya; Alhaji dan Asabe Tela ya zo na biyu; sai Alhaji Sani Dala ya zo na uku.
Da yake yi wa Aminiya karin bayani, a karshen makon da ya gabata a ofishin kungiyar da ke gidan dirama na Agumalu, sabon shugaban kungiyar, Alhaji danladi Zage ya yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana. Ya gode wa Allah da Ya ba shi nasara kuma ya roki Ya ba shi karfin halin gudanar da shugabanci nagari a kan adalci.
Ya ce an zabi Latifa Akindobi, wacce ta kada Maryam Amukoko, a matsayin shugabar mata ta kungiyar. “A al’adar kungiyar idan aka zabi shugaba, shi yake zabar sauran wadanda za su rike sauran mukaman kungiyar. Saboda haka nan ba da jimawa ba zan bayyana sunan mutanen da nake so mu yi aiki tare da su.
“Na tsara ayyuka da dama muhimmai da nake son gudanarwa don bukasa kungiyar, wadanda suka hada da ziyarce-ziyarcen masallatai da manyan mutane da makabartu da kuma hada kai da ’yan jarida da gidajen rediyo don yada kungiyar a ko’ina a kasar nan”. Inji shi.
Ya yi alwashin bullo da sabbabin ayyukan cigaba a kungiyar tare da gudanar da mulki ba tare da nuna bambanci ba a tsakanin mambobin kungiyar.
’Yan kungiyar da dama da Aminiya ta tattauna da su sun yi na’am da zaben sabon shugaban kungiyar.