‘kungiyarmu na wayar da kan Fulani makiyaya’
Shugaban kungiyar Kautal Hore reshen Jihar Neja Alhaji Bello Garatu ya ce kungiyarsu tana wayar da kan Fulani makiyaya game da abin da ya shafi sha’anin rayuwa da kuma yadda za su rika mu’amala da sauran al’umma.Garatu ya yi wannan bayani ne a wata hira da wakilin Aminiya a lokacin da ya kai ziyarar sada […]
Shugaban kungiyar Kautal Hore reshen Jihar Neja Alhaji Bello Garatu ya ce kungiyarsu tana wayar da kan Fulani makiyaya game da abin da ya shafi sha’anin rayuwa da kuma yadda za su rika mu’amala da sauran al’umma.
Garatu ya yi wannan bayani ne a wata hira da wakilin Aminiya a lokacin da ya kai ziyarar sada zumunci ga Fulani makiyayan garin Benin da ke Jihar Edo a kwanakin baya.
Ya ce: “kungiyarmu ta fi mayar da hankali ne a kan abin da ya shafi ilimantar da Fulani makiyaya da suka fi zama a daji. Mukan fahimtar da su muhimmancin rayuwa da hadin kai da zaman lafiya da bin doka da oda.”
Ya ce, babban abin da suka sanya a gaba shi ne, ganin Fulani makiyaya sun fahimci yadda rayuwa take da kuma tabbatar da sun rungumi zaman lafiya, sannan suna kokarin wayar da kansu don su daina gaba, su hada kai da juna da gwamnati da kuma manoma.
“Abin da ya fi cutar da Fulani a wannan zamanin shi ne jahilci, domin manyansu da kananansu ba sa zuwa makaranta, suna ganin kiwon dabbobinsu a daji ya fi komai zama alheri gare su. Na biyu, Fulani na kara nisantar gwamnati ballantana ta fahimci damuwarsu, hakan ya sanya suka zama kamar saniyar ware.” Inji shi.
Ya ce, kungiyarsu ta kakkafa makarantu na zamani domin ’ya’yan Fulani su samu ilimin addini da na zamani tare da wayar musu da kai a kan abubuwa masu muhimmanci, sannan sukan sasanta rikicin da ke tasowa tsakanin fulanin da manoma.
Ya ba manoma da makiyaya shawara a kan su hada kai don a samu dauwamammen zaman lafiya.
“Makiyaya da manoma mutane ne da babu yadda wani zai zai raba zamansu, domin da gona da dabbobi duk a daji suke, sai dai kawai a bukaci masu dabbobin su daina yi wa masu gonaki barnar ganganci, kuma idan aka samu kuskure a yi gaskiya da adalci a biya masu gonaki hakkinsu, don haka ko wani bangare su bar daukar doka a hannunsu.
“A duk lokacin da wani abu ya faru tsakanin fulani da manoma, to gwamnati ta bi diddigi don gano mai gaskiya, sannan ta yi adalci wajen hukunta duk mai laifi. Ina fata Ardo-Ardo za su rika shirya tarurruka wayawar wa jama’arsu kai dangane da muhimmancin zaman lafiya.” Inji shi.