kungiyarmu ta masu sayar da katako na da membobi sama da dubu biyar – Alhaji Mani Dogo

Mataimakin  shugaban kungiyar masu sayar da katako ta Jihar Sakkkwato Alhaji Mani Dogo kuma Dan siyasa dake shugabantar jam’iyar APC a karamar hukumar Silame ya ce suna da membobi dubu biyar da dari biyar a kungiyarsu da ke sana’ar sayar da katako da sarrafa shi a kasuwar kara da ke jihar.  Alhaji Mani ya yi […]

kungiyarmu ta masu sayar da katako na da membobi sama da dubu biyar – Alhaji Mani Dogo

Mataimakin  shugaban kungiyar masu sayar da katako ta Jihar Sakkkwato Alhaji Mani Dogo kuma Dan siyasa dake shugabantar jam’iyar APC a karamar hukumar Silame ya ce suna da membobi dubu biyar da dari biyar a kungiyarsu da ke sana’ar sayar da katako da sarrafa shi a kasuwar kara da ke jihar. 

Alhaji Mani ya yi wannan kalamai ne a zantawarsa da Aminiya a shagonsa da ke cikin kasuwar karar, inda ya ce abin da ya ja ra’ayinsu ga kafa kngiyar, shi ne yadda masu sana’ar suka yawa har aka fara samun rashin fahimta a tsakaninsu da, sai suka ga ba su da wata hanya kamar su hada kansu wuri daya don ciyar da sana’ar da Jihar Sakkwato baki daya a gaba don akwai alheri cikin dunkulewa.

“A kungiyarmu ba mu da wata matsala, ana bai wa kowa hakkinsa da damarsa ta aiki da taimakon juna da yi wa kanmu gyare-gyaren da ya kamata mu yi a domin taimakon sana’armu, kum muna girmama junanmu. Ba ka samu an raba fada a tsakaninmu domin dokarmu na aiki.

“A kasuwar Katako ba mu da wani cikas a kasuwancinmu yana tafiya daidai ita sana’a, amfaninta ya fi hasararta, a yanzu kasuwarmu kullum sai tirela 10 ta zo shake da katako, a haka ake saukewa kuma mu sayar, da gwamnati za ta tallafa mana da bashi a kungiyarmu da za mu kara janyo matasa cikin kasuwancin da har membobinmu za su kai miliyan nan take.” A cewar Dogo.

Da ya juya kan batun tayar da su da gwamnati ke kokarin yi daga wurinsu zuwa wani waje daban ya ce duk wanda yake gidansa zaune lafiya baya son a canja masa wuri, amma idan ita gwamnati take son yin haka ba mu da zabi, ita ta fi sanin abin da ya fi daidai a wurinsu fatarsu tashin ya zama mana alheri.

Kan bashin da gwamnatin Sakkwato za ta bai wa ’yan kasuwa kunwa, sai ya ce “ba mu cewa ba mu ciki don muna tafiya tare da shugaban ’yan kasuwa ne kuma ya tabbata mana komai gwamnati za ta bayar muna cikinsa,” in ji Mani Dogo. 

Daga karshe, Alhaji Mani ya yaba wa kungiyar sanatocin Arewa bisa nada Sanata Wamakko a matsayin shubaba.

“Na san ya cancanta domin jarumi ne kwarai. Kowane matsayi ya samu ba zan ce ya masa girma ba, kuma na gamsu da yadda hulda da mutunta juna ke tafiya tsakaninsa da Gwamna Tambuwal don ciyar da Sakkwato. Zama lafiya ya fi komai,” a cewar Alhaji Mani.