kungiyarmu ta samar da cigaban Kano ta Arewa ce – Sa’in Kano
Shugaban kungiyar Cigaban Kano ta Arewa, watau ‘Kano North Debelopment Forum’ kuma hakimin Makoda, Dokta Wada Waziri Sa’in Kano, ya ce an kafa wannan kungiya ce domin a hada hannu wajen samar da ci gaba mai kyau a shiyyar Arewacin Kano, wadda ta kunshi jimlar kananan hukumomi 13. Ya yi wannan bayani ne a ganawarsu […]
Shugaban kungiyar Cigaban Kano ta Arewa, watau ‘Kano North Debelopment Forum’ kuma hakimin Makoda, Dokta Wada Waziri Sa’in Kano, ya ce an kafa wannan kungiya ce domin a hada hannu wajen samar da ci gaba mai kyau a shiyyar Arewacin Kano, wadda ta kunshi jimlar kananan hukumomi 13.
Ya yi wannan bayani ne a ganawarsu da wakilinmu, inda ya ce wannan kungiya babu ruwanta da siyasa, ta kafu ne tun kimanin shekaru biyu da suka gabata bisa manufofin bada gudummawa wajen cigaban wannan shiyya ta Arewacin Kano, don haka ya sanar da cewa ayyukan kungiyar za su cigaba da kasancewa na hidimar al’umma ta hanyoyi daban-daban.
Dokta Wada Waziri ya kuma sanar da cewa kafin a kafa kungiyar sai da aka tsara mata kundin tsarin mulki, sannan aka yi mata rajista ta yadda za ta kasance a bisa kyakykyawan ginshiki wanda kowa zai amfani kafuwarta da aikace-aikacenta a wannan yanki ba tare da gajiyawa ba.
Bugu da kari, Sa’in na Kano ya bayyana cewa duk wanda ya dubi tarihin kafa wannan kungiya ko shakka babu zai fahimci cewa ta zo ne bisa tsari da manufofi masu amfani ga al’umar wannan shiyya da Jihar Kano har ma da kasa baki daya. Don haka ya bukaci al’umma a ko’ina suke da su sani cewa an kafa kungiyar ne sakamakon tunani mai kyau da akayi domin kishin cigaban yankin.
Haka kuma ya yi fatan cewa al’ummar yankin zasu kara daukar kungiyar da matukar muhimmanci saboda irin fuskokin dake cikinta wadanda dukkaninsu mutane ne masu mutunci da kuma sanin ya kamata, inda ya hori al’umar dake shiyyar Kano ta Arewa da su dauki kungiyar a matsayin jagora ta kowane fanni na zamantakewa.
Dokta Wada Waziri, Sa’in Kano ya jaddada cewa kungiyar tasu za ta bullo da sabbin shirye-shirye da bada kulawa ta musamman ga fanin kula da lafiya da ilimi da tsaro da kuma kasuwanci ta yadda kowa zai amfana da ayyukanta cikin nasara, sannan ya godewa daukacin mamboin kungiyar da kuma fatan Ubangiji Ya kara mana lafiya da zaman lafiya a wannan kasa tamu mai albarka.