Kungiyoyi na karo-karon saya wa Zulum fom din tazarce N50m

Suna so Zulum ya sake tsayawa takara a jam’iyyar APC

Kungiyoyi na karo-karon saya wa Zulum fom din tazarce N50m

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum

Wasu kungiyoyi 150 a Jihar Borno sun hada kai don saya wa Gwamna Babagana Umara Zulum fom din sake tsayawa takara kan Naira miliyan 50.

A cewar wani rahoto, kungiyoyin sun nemi Gwamna Zulum ya sake tsayawa takara a karkashin jam’iyyar APC ranar Juma’a a Maiduguri, baban birnin jihar.

Kakakin kungiyoyin, Umar Shettima, ya ce sun bukaci Zulum ne da ya ci gaba da rike mukaminsa bisa la’akari da ayyukan da ya yi a dukkanin bangarori a wa’adinsa na farko bisa jagorancin jihar. 

Shettima wanda  kuma shi ne Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Kasa Reshen Jihar Borno, ya ce “Kungiyoyi masu rajista ne suka hada gwiwa tare da kwararrun malamai, bangaren kiwon lafiya, tallace-tallace, sufuri da kungiyoyin mata da sauran su don aiwatar da wannan kuduri. 

“Muna da kudurin tabbatar da cewa Farfesa Babagana Umara Zulum ya ci gaba da zama a ofis, bayan da ya kawo irin nasarorin da ba a taba gani ba a duk fannonin rayuwa cikin shekara uku kacal a kan mulkin Jihar Borno. 

“Muna kira gare shi da ya sake tsayawa takara karo na biyu domin ya ci gaba da ayyukan alheri da yake yi wa mutanen Borno.

“Kungiyoyin sun yanke shawarar siyan fom din ne don nuna sha’awa da neman tsayawa takarar Gwamna Zulum a zaben 2023,” inji Shettima.

Ya kuma bukaci al’ummar Borno su ma su bayar da goyon bayansu ta hanyar bayar da gudumawa a wani asusu na musamman, wanda za a bayyana bayanansa daga baya domin ana bukatar kudi don yakin neman zaben da ke tafe.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50