Kungiyoyi sun goyi bayan Goje a matsayin shugaban majalisa

Kungiyar tuntubar juna ta shiyyar Arewa maso Gabas (NECF) da wasu kungiyoyi 5, sun bukaci Sanata Danjuma Goje, daya nemi mukamin shugaban majalisar dattawan Najeriya. Kungiyoyin sun fitar da wannan matsaya ne, bayan wani taron gaggawa da suka gudabar a otal din Zaranda a garin Bauchi jiya Laraba, inda suka  nemi Sanata Goje da ya […]

Kungiyoyi sun goyi bayan Goje a matsayin shugaban majalisa

Sanata Muhammad Danjuma Goje

Kungiyar tuntubar juna ta shiyyar Arewa maso Gabas (NECF) da wasu kungiyoyi 5, sun bukaci Sanata Danjuma Goje, daya nemi mukamin shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Kungiyoyin sun fitar da wannan matsaya ne, bayan wani taron gaggawa da suka gudabar a otal din Zaranda a garin Bauchi jiya Laraba, inda suka  nemi Sanata Goje da ya hamzarta bayyana bukatarsa ta neman kujerar. Sauran kungiyoyin 5 sun hada da Kungiyar Dattawan Shiyyar, Shugaban Matasa na jamiyar APC da kungiyoyin siyasa a jihar Gombe da ta Gamayyar tautaunawa ta Borno da dai sauransu.