kungiyoyi sun shirya taro kan sha’anin kudi

kungiyar mataimakan shugabannin jami’o’i wacce ake kira AbCNU da hadin gwiwar cibiyar nazarin akantoci ta ICAN sun shirya taron kwanaki biyu don fadakar da membobinsu yadda za su gudanar da sha’anin kudin jami’o’insu ba tare da wata matsala ba.  Taro mai taken “Sha’anin tafiyar da kudin jami’a ba tare da matsala ba” ya gudana ne […]

kungiyoyi sun shirya taro kan sha’anin kudi
kungiyoyi sun shirya taro kan sha’anin kudi

kungiyar mataimakan shugabannin jami’o’i wacce ake kira AbCNU da hadin gwiwar cibiyar nazarin akantoci ta ICAN sun shirya taron kwanaki biyu don fadakar da membobinsu yadda za su gudanar da sha’anin kudin jami’o’insu ba tare da wata matsala ba. 

Taro mai taken “Sha’anin tafiyar da kudin jami’a ba tare da matsala ba” ya gudana ne a Abuja, a karshen makon da ya gabata.
Da yake jawabin bude taron, Tsohon Shugaban Cibiyar Akantoci ta Najeriya, Titus Soetan ya ce taron zai amfanar da wadanda suka halarce shi wajen lakantar tafiyar da kudin jami’o’insu.
Soetan wanda shi ne shugaban cibiyar akantoci na 52 ya bayyana cewa cibiyar ta dade tana goyon bayan duk wani ci gaban da yake kan turbar ilimi.
Hakan a cewarsa shi ya sanya cibiyar ta gina dakunan karatu a wasu jami’o’i da manyan makarantun kasar nan.
Ya bayyana cewa cibiyar ta bayar da tallafin karatu ga daliban da suka zama zakaru a fannin akanta da kuma wadanda suka karanta wasu fannoni da suke son su zama akantoci.
Da yake jawabi, Sakatare Janar na kungiyar Mataimakan Shugabannin Jami’o’in Najeriya, Farfesa M.O Faborode ya bayyana cewa taron ya dace kuma yana da muhimmanci.
Ya bayyana cewa taron zai zama wata kafa da mahalartansa za su koyi yadda za su tafiyar da kudin jami’o’insu ba tare da wata mushkila ba.
Farfesa Faborode ya bayyana mataimakan shugabannin jami’o’i a matsayin babbar na’urar da ke tafiyar da jami’o’i.
Sai ya bukace su su rika kokarin hada kan wadanda suke aiki a karkashinsu don cimma burin da ake so.
Da yake karin bayani, kwararren akanta, Farfesa Francis Ojaide ya bayyana cewa karancin kudi, karancin ma’aikata da kuma nuna halin ko-in-kula a lokacin aiki na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo rashin fahimtar juna a jami’o’i.