‘kungiyoyin aikin gayya suna kawo bunkasar kiwon lafiya’
Shugaban Kwamitin koli na kungiyoyin Aikin Gayya na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Garba Aminu kofar Na’isa, ya ce kungiyoyin aikin gayya suna taimakawa wajen bunkasa kiwon lafiya da tsaftace muhalli a birane da kuma yankunan karkara.Ya yi wannan bayani ne lokacin da ya duba yadda kungiyoyin aikin gayya suka gudanar da wasu aikace-aikace na yashe […]
Shugaban Kwamitin koli na kungiyoyin Aikin Gayya na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Garba Aminu kofar Na’isa, ya ce kungiyoyin aikin gayya suna taimakawa wajen bunkasa kiwon lafiya da tsaftace muhalli a birane da kuma yankunan karkara.
Ya yi wannan bayani ne lokacin da ya duba yadda kungiyoyin aikin gayya suka gudanar da wasu aikace-aikace na yashe magudadu da yin ciko kan hanyoyin ruwa domin yin rigakafi kan yawaitar ambaliyar ruwa da ake samu musamman a birane.
Ya ce a duk shekara sai an samu ambaliyar ruwa wadda take rusa gidaje da kuma lalata hanyoyi, “don haka yana da kyau kungiyoyin aikin gayya su kara zage damtse wajen ci gaba da gyaran muhalli da kuma yashe magudadun ruwa tun kafin faduwar damina.”
Alhaji Ibrahim kofar Na’isa ya bayyana jin dadinsa game da yadda kungiyoyin aikin gayya da ke Jihar Kano suke “kokari kwarai da gaske” duk da irin karancin kayan aikin da suke da shi, sannan suna taimakawa gwamnati wajen tabbatar da ganin shirin tsaftar muhalli duk karshen wata yana tafiya cikin nasara.
Hakazalika, ya ce ayyukan kungiyoyin suna da muhimmanci, don haka ya bukaci gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ta dauki matakai domin ganin kungiyoyin aikin gayya da ke fadin jihar suna samun kulawa ta musamman ta yadda za su ji dadin gudanar da ayyukansu na taimakon kai da kai.
Har ila yau, shugaban kwamitin kolin ya gode wa daukacin kungiyoyin aikin gayya da ke jihar da ma’aikatar kula da muhalli da kuma hukumar kwashe shara ta jihar saboda yadda aka hada hannu wajen aikin tsaftace jihar.