Kungiyoyin da ke buga gasar Firimiyar Ingila za su daina tallan kamfanonin caca
Matakin zai fara aiki ne daga kakar 2025/2026
Kungiyoyin kwallon kafar da ke buga gasar Firimiya a kasar Ingila sun ce daga karshen kakar shekara ta 2025/2026 za su daina sanya tallan kamfanonin caca a rigunansu.
Yanzu haka dai takwas daga cikin manyan kungiyoyi 20 da ke fafata gasar na dauke da irin wadannan tallace-tallacen a jikin rugunan nasu.
Hukumar ta gasar Firimiyar ce dai ta sanar da daukar matakin a ranar Alhamis, inda ta ce za a dauki shekara ukun ne kafin a fara daukar matakin domin a ba sauran kungiyoyin da ke da tallace-tallacen damar kammala yarjejeniyar.
Sanarwar ta ce, “A yau, kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya sun amince da murya daya cewa za su daina sanya tallace-tallacen kamfanonin caca a jikin rigunansu, inda suka zama gasa ta farko a Ingila da ta dauki wannan matakin domin rage tallan caca.
“Sanarwar ta biyo zuzzurfar tattaunawa da kungiyoyin da dukkan sauran masu ruwa da tsaki da kafafen yada labarai, a matsayin wani matakin gwamnati na yi wa dokokin caca kwaskwarima,” in ji sanarwar.
Tuni dai a kasashen Spain da Italiya aka haramta tallan kamfanonin a jikin rigunan wasannin.
Yanzu haka dai kungiyoyin Bournemouth da Brentford da Everton da Fulham, Leeds da Newcastle da Southampton da West Ham na tallata irin wadannan kamfanonin.