kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi taro a Bauchi

kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi taro domin gano maslahar da za a shawo kan matsalar cin zarafin jama’a da ake zargin jami’an tsaro da aikawa a wasu lokuta yayin da suke gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na kasar nan.Taron ya gudana a dakin taro na DEC, inda aka gayyaci jami’an tsaro na ’yan […]

kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi taro a Bauchi

kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi taro domin gano maslahar da za a shawo kan matsalar cin zarafin jama’a da ake zargin jami’an tsaro da aikawa a wasu lokuta yayin da suke gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na kasar nan.
Taron ya gudana a dakin taro na DEC, inda aka gayyaci jami’an tsaro na ’yan sanda da na gidan yari da na tsaron farin kaya da lauyoyin ba da tallafin shari’a da kuma kungiyoyi masu ruwa da tsaki game da abin da ya shafi kare hakkin dan Adam da taimakon gaggawa da hukumomin jin dadin jama’a na jiha da tarayya da kananan hukumomi.
Taron ya gudana a karkashin kungiyoyin kare hakkin dan Adam na ‘Search For Common Ground’ da ‘Bauchi Human Right Network’, inda aka tattauna don samun mafita game da yadda mutane ke fuskantar cin zarafi a lokutan da wani abu ya hada su da jami’an tsaro, lamarin da ke kai ga rasa rayukan jama’a da kuma shiga cikin mawuyacin hali.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna