Kungiyoyin kwadago sun janye yajin aiki
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC sun janye yajin aikin gama garin da suka shirya farawa a yau Talata. Wannan ya biyo bayan yarjejeniyar da kungiyoyin suka cimma da masu ruwa da tsaki a tattaunawar da suka yi a kan batun karin mafi karancin albashin ma’aikata na naira dubu 30 wanda aka yi a daren ranar Litinin. […]
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC sun janye yajin aikin gama garin da suka shirya farawa a yau Talata.
Wannan ya biyo bayan yarjejeniyar da kungiyoyin suka cimma da masu ruwa da tsaki a tattaunawar da suka yi a kan batun karin mafi karancin albashin ma’aikata na naira dubu 30 wanda aka yi a daren ranar Litinin.
Shugaban kungiyar NLC na Najeriya Ayuba Wabba ne ya sanar da janyewar yajin aikin.