Kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aiki a Faransa
Koyaushe muna cewa za mu shiga yajin aiki mafi girma idan ya cancanta.
A Talatar nan ce kungiyoyin kwadago a Faransa suka sake fitowa don kalubalantar shugaba Emmanuel Macron ta hanyar shirya yajin aiki da kuma zanga-zanga, don nuna rashin amincewa da garambawul din da ya yi wa tsarin fanso na kasar.
Kungiyoyin sun sha alwashin tsaida al’amura cik a kasar, bayan kudirin shugaban na kawo sauye-sauye a tsarin fansho da ya kunshi kara shekarun yin ritaya daga 62 zuwa 64 da kuma tsawaita shekarun kudin da za a rinka cire wa ma’aikaci na fansho.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta CFDT, Laurent Berger, a lokacin ganawarsa da Radio Faransa, ya yi kira ga dukkanin ma’aikata da ‘yan kasar da kuma ‘yan fansho su yi turu-ruwa wajen fitowa zanga-zangar.
Ya ce ba zai yiwu shugaban kasar ya ci gaba da yin burus da bukatun masu zanga-zangar ba.
Shirin kwaskwarima ga tsarin fansho na cikin kudurorin da shugaba Macron ya gudanar da yakin neman zabe akai a lokacin yakin neman sake zabensa a shekarar da ta gabata, wanda ‘yan majalisarsa ke ganin ya zama wajibi a yi hakan don kare shirin fanshon kasar daga durkushewa.
Sai dai suna funskantar turjiya daga bangaren Majalisar Dokoki da kuma al’ummar kasar, inda kusan mutum biyu a duk cikin mutum uku ke nuna rashin amincewa da shi.
Kungiyoyin sun ce yajin aikin na yau Talata zai gurgunta sha’anin sifuri na kasar, inda ‘yan sanda ke sa ran kimanin mutane miliyan daya da dubu dari daya zuwa da dubu dari hudu ne za su gudanar da zanga-zangar a wurare kusan 260 a fadin kasar.
A baya-baya nan an gudanar da zanga-zanga daban-daban har sau biyar a sassan kasar, sai dai wannan makon zanga-zangar ta zo ne da sabon salo wato tsakanin gwamnati da masu adawa da sauye-sauyen da ake son bijiro wa tsarin fansho.
“Koyaushe muna cewa za mu shiga yajin aiki mafi girma idan ya cancanta,” a cewar shugaban kungiyar masu ra’ayin rikau na CGT, Philippe Martinez, da yake shaida wa jaridar Journal du Dimanche ranar Lahadi.
Tun a jiya Litinin an tsammanin fiye da kungiyoyi 260 za su fito a fadin kasar, kama daga birane zuwa kauyuka, inda suke adawa da sake fasalin tsarin ‘yan fansho.
Bayanai sun ce yajin aikin zai shafi harkokin sufuri da bangaren makamashi da ayyukan jama’a.
’Yan sanda na sa ran mutane miliyan 1.5 za su mamaye titunan kasar.
Idan wannan kiyasin ya zama gaskiya, wannan Talatar na iya zama ranar zanga-zanga mafi girma a cikin shekarun da suka gabata, inda a baya mutane miliyan 1.27 da suka halarci zanga-zangar a ranar 31 ga Janairu, kuma ta zarce zanga-zangar garambawul ta fansho a 2010.