kungiyoyin mata sun nuna bakin ciki kan yadda ake cin zarafin mata a Borno

Kungiyoyin mata a Jihar Borno sun nuna bakin ciki da damuwa game da yadda ake yawan samun fyade da garkuwa da mutane da cin zarafin mata a Jihar Borno. Shugaban kungiyar Mata ’Yan Jarida ta kasa (NAWOJ) reshen Jihar Borno, Hajiya Hadiza Bukar ce ta jagoranci kungiyoyin matan inda suka gabatar da taron manema labarai […]

kungiyoyin mata sun nuna bakin ciki kan yadda ake cin zarafin mata a Borno

Kungiyoyin mata a Jihar Borno sun nuna bakin ciki da damuwa game da yadda ake yawan samun fyade da garkuwa da mutane da cin zarafin mata a Jihar Borno.

Shugaban kungiyar Mata ’Yan Jarida ta kasa (NAWOJ) reshen Jihar Borno, Hajiya Hadiza Bukar ce ta jagoranci kungiyoyin matan inda suka gabatar da taron manema labarai a garin Maiduguri, don nuna bakin ciki kan abin da ke faruwa.

A cewar Hajiya Hadiza Bukar, “A gaskiya a matsayinmu na mata iyayen al’umma mun yi tir da Allah wadai da watsa wa Fatima Habu Usman ’yar shekara 26 kuma daliba a ajin karshe a Jami’ar Maiduguri a fannin koyon aikin Nas da Ungzoma guba a makon jiya bayan ta hau Keke NAPEP  a wannan gari na Maiduguri. Gaskiya wannan abin bakin ciki ne matuka domin babu abin da yarinyar ta yi musu. Kadan ya rage al’umma ta fara cin moriyarta sakamakon karatun da take shirin kammalawa sai kawai su aikata mata wannan danyen aiki. Wannan rashin imani ne.”

“Shi ya sanya muka yanke shawarar fada wa duniya cewa ba mu ji dadin wannan al’amari ba kuma muna Allah wadai da duk wanda ya aikata wannan mummunan aikin domin  mace ce ta haife shi kuma idan aka yi wa wata ’yar uwarsa hakan ba zai ji dadi ba. don haka muna kira da babban murya cewa duk mai yin wannan ya tuba ya bari, idan ba haka ba za mu shiga gudanar da addu’o’i a masallatai da majami’u domin ganin bayansu, kuma muna kira ga hukumomin tsaro su yi wa Allah su fadada bincike don dakile aukuwar haka a gaba,” inji ta.

da ta juya ga su masu aiki da Keke NAPEP, ta shawarce su su duba tsarin yadda suke ba kowane mutum aikin da su ba tare da bin ka’ida ba, “Wajibi ne mutanen da suka mallaki Keke NAPEP su rika duba cancanta da sanin ya kamata da sanin halin mutum kafin su dauki dukiyansu su ba shi. Su ma Shugabannin kungiyar ’Yan Keke NAPEP ya kamata su rika gudanar da bincike don su tantance mutanen kirki da na banza a cikinsu domin gudun kada su shafa musu kashin kaji,” inji ta.