‘kungiyoyin matasa su kasance na matasa ba matasan-kai ba’
An bukaci matasa da a kowane lokaci su kasance matasan ne, ba matasan-kai ba, wadanda za a rika amfani da su a lokacin da ake bukata, karshe a yi watsi da su bayan bukata ta biya. Alhaji Sani Lawal Bakin-kasuwa ne ya yi wannan kira a lokacin da wata kungiyar hadin gwiwa a tsakanin Najeriya […]
An bukaci matasa da a kowane lokaci su kasance matasan ne, ba matasan-kai ba, wadanda za a rika amfani da su a lokacin da ake bukata, karshe a yi watsi da su bayan bukata ta biya.
Alhaji Sani Lawal Bakin-kasuwa ne ya yi wannan kira a lokacin da wata kungiyar hadin gwiwa a tsakanin Najeriya da Nijar, mai suna ‘Taghlamt’ ta ziyarce shi a ofishinsa da ke Katsina a farkon wannan makon, a matsayinsa na daya daga cikin iyayen kungiyar da ke Najeriya.
Alhaji Sani ya tunasar da matasan su yi la’akari da cewa duk wani cigaban da kowace irin kasa ke takama da shi, yakan fito ne daga kokarin matasa ne, amma kuma wani abin bakin ciki, sai ya kasance su ne koma-baya, “Domin ana mayar da mu tamkar matasan-kai a lokacin kwanciya barci. Da zarar an tashi bullo da wani shiri za ka ji an ce a nemo matasa, amma karshe in ba a yi sa’ar shugabanci na adalci ba, sai a bar mu, ko dai muna fada da juna, ko mu fada sace-sace ko ayyukan ta’addanci da sauran makamantan haka”. Inji shi.
Alhaji Sani ya cigaba da jan hankalin matasan da akowane lokaci su rika hada kansu ta hanyar kafa kungiyoyi wadanda suke da rajistar gwamnati domin bambanta kansu da bata-gari.
A karshe ya yaba da kokarin da aka yi na haduwa a tsakanin kasashen biyu, wadanda ba wai masu makwabtaka da juna kawai ba ne, a’a, ’yan uwa ne.
Tun farko sai da wakilin shugaban kungiyar ta ‘Taghlamt’, mai ma’anar ‘Matafiya’, Alhaji Yazeed Nasudan ya bayyana cewar sun kawo ziyarar ce don girmamawa da kuma kara sada zumunci, wanda zai taimaka wa hada kai a tsakaninta da sauran kungiyoyi, kuma a bayyana wa jama’a manufofi da kudurorin kungiyar.
Alhaji Yazeed ya yi na’am da kyakkyawar tarba da kuma karbar da aka nuna musu, lamarin da ya ce ya kara musu natsuwa da jin dadin gudanar da al’amuran da suka kawo su.
A karshe ya ce kofar kungiyar a bude take ga duk wanda yake da kyakkyawar manufar ganin cigaban al’umma a kowane lokaci.