Kungiyoyin Najeriya da za su fafata wasannin Afirka
Rivers United kungiya ce da aka hade kungiyoyin Dophins FC da Sharks FC a shekarar 2016.
A Nahiyar Afirka, akwai manyan wasanni biyu, wato Gasar Zakarun Afirka (CAF Champions League) da ta CAF Condeferations da ake bugawa duk shekara.
Ana gasa biyun ne maimakon gasa uku da ake fafatawa a Turai, bayan an kirkiri ta uku a shekara biyu da suka gabata.
Kungiyar da ta lashe Gasar Firimiya ta Najeriya da ta biyu ne suke wakiltar kasar a Gasar Zakarun Afirka, sannan ta uku da ta hudu su je Confederations.
Kungiyar Enyimba International ta Jihar Abiya ce ta lashe gasar Firimiyar Najeriya a bara, wanda hakan ya sa ta shige gaba zuwa gasar Zakarun Afirka.
Sai kungiyar da ta zo ta biyu, wato Remo Stars. Ke nan su ne za su wakilci kasar nan a bana.
Tsohon dan wasan Najeriya, Finidi George ne yake horar da ’yan wasan Kungiyar Enyimba, inda ya taimaka wajen dawo da martabar kungiyar bayan ta yi kasa na tsawon lokaci.
Kungiyar ta lashe Firimiyar Najeriya sau tara; a shekarun 2001, 2002, 2003, 2005, 2007, 2009-10, 2015, 2019 sai a bana 2023.
Haka kuma ta lashe Kofin Kalubale sau hudu; a shekarun 2005, 2009, 2013 da 2014.
A Gasar Zakarun Afirka kuwa, kungiyar ta Enyimba ta lashe kofin sau biyu a jere a shekarar 2003 da 2004, sannan ta lashe gasar kece-raini wato CAF Super Cup sau biyu a shekarar 2004 da 2005.
Har yanzu kungiyar ce kungiyar Najeriya mafi daraja a Afirka kasancewar ta fi daga darajar kasar nan a gasar, sannan ta fitar da zaratan ’yan wasa.
Daga cikin zaratan ’yan wasan da suka lashe gasar Zakarun Turai a kungiyar, har da tsohon Golan Najeriya, Vincent Enyeama da Dele Ayenugba da sauransu.
Sannan a bana kungiyar ta sanar da tsohon Kyaftin din Super Eagles Nwanko Kanu a matsayin sabon shugaban kungiyar.
Hakan ya sa ake tunanin kungiyar za ta taka rawar gani a gasar da za a a fara a watan Agusta mai zuwa.
A bangaren Kungiyar Remo Stars, ana ganin kungiyar ta shirya tsaf ganin yadda ta yi tsari mai kyau, musamman wajen lura da ’yan wasanta.
A gasar Firimiyar bara kungiyar ta bayar da mamaki, inda sai ta buga wasa tara a jere ba a doke ta ba. Sannan ta ci gaba da dagewa don lashe gasar.
A bangaren kofin Confederations kuwa, Kungiyar Rivers United da Bendel Insurance FC ne za su wakilci Najeriya.
Rivers United kungiya ce da aka hade kungiyoyin Dophins FC da Sharks FC a shekarar 2016 suka zama Kungiyar Rivers United, inda ta fara tashe.
Daya kungiyar ita ce Kungiyar Bendel Insurance, wadda tsohuwar kungiya ce, amma ta samu koma-baya na tsawon lokaci kafin ta farfado a yanzu.