kungyar ‘yan kasuwa nakasassu ta yaba wa ministan Abuja

kungiyar ‘yan kasuwa nakasassu reshen Abuja ta yaba wa Ministan Abuja bisa yadda yake saka su cikin tsare-tsaren gwamnati. Wannan sanarwar ta fito ne a wata takarda da shuban kungiyar da sakarensa suka sanya wa hannu, inda suka nuna matukar godiyarsu da jin dadinsu ga ministan bisa yadda yake lure da lamuran su kamar ‘ya’yanshi […]

kungyar ‘yan kasuwa nakasassu ta yaba wa ministan Abuja

kungiyar ‘yan kasuwa nakasassu reshen Abuja ta yaba wa Ministan Abuja bisa yadda yake saka su cikin tsare-tsaren gwamnati.

Wannan sanarwar ta fito ne a wata takarda da shuban kungiyar da sakarensa suka sanya wa hannu, inda suka nuna matukar godiyarsu da jin dadinsu ga ministan bisa yadda yake lure da lamuran su kamar ‘ya’yanshi da ya haifa.

A cewar su “Muna godiya bisa yadda kake nuna mana cewa muma mutane ne kamar kowa, lokacin da muka ziyarce ka, ka tarbe mu hannu biyu-biyu kamar ‘ya’yank na ciki, gwamnatin ka ta nuna mana soyayya da kauna.

“Hakanan kuma muma godiya bisa abubuwan da ka mana a baya, sannan kuma muna jiran sauran alkawuran da ka dauka a kan wannan kungiyar ta mu,” kamar yadda takardar ta nuna.

Hakanan kuma, ‘ya’yan kungiyar sun yaba wa sakataren harkokin tallafi na ofishin minstan bisa yadda ta karbe su, inda suka ce “Muna so mu yi amfani da wannan damar wajen fada maka cewa sakataren harkokin tallafa wa mutane a ofishinka tana da tausayi da hakuri, kuma ta dauke mu tamkar ‘ya’yanta. Ba ta muzguna mana, kuma tana duk mai yiwu wa wajen ganin cewa muma mun zama ‘ya’ya tamkar sauran ‘ya’ya.

“Don haka ne muke kira gare ka da karrama ta domin ya zama izina ga sauran ma’aikata. Hakan zai sa sauran su dage wajen yin aikin su yadda ya kamata da kuma taimakon mutane.

“Mun gode, Allah Ya kara daukaka.”