Kunkuru na yi wa Bushiya qafa
A Najeriya abu ne mai sauqi a ga ubangida da kuma dan gidansa a siysance sun samu rashin jituwa bayan dayansu ya cicciba gudan hawa mulkin da zai ba shi damar rufa masa asiri, amma daga bisani sai a gan su a rana, sun rabu baram-baram. Irin abin da ya wakana ke nan tsakanin Cif […]
A Najeriya abu ne mai sauqi a ga ubangida da kuma dan gidansa a siysance sun samu rashin jituwa bayan dayansu ya cicciba gudan hawa mulkin da zai ba shi damar rufa masa asiri, amma daga bisani sai a gan su a rana, sun rabu baram-baram. Irin abin da ya wakana ke nan tsakanin Cif Olusegun Obsanjo da kuma Cif Goodluck Jonthan. Masu lura da al’amuran siyasar qasar nan sun tabbatar da cewa muzantawar da tsohon shugaban qasa, Cif Obasanjo ya yi wa Jonathan na daga cikin abubuwan da suka zaizaye masa mutunci a idanun qasashen qetaren da suke dasawa da Obasanjo, a matsayinsa na babban dan-korensu, kuma idanunsu da kunnuwansu, kan dukkan abubuwan da ke wanzuwa a cikin qasar da kuma fadar gwamnati. Mista Goodluck Jonathan ya haqure da dukkan tozartawar da Obasanjo da maqararrabansa suka yi masa, ya kuma tabbatar hakan ne ya janyo masa faduwa warwas a zabe, amma bai fito fili ya amayar da takaicinsa game da haka ba, bai kuma mayar da martani ba, ya bar komai a cikinsa, domin ya yi amanna cewa ba domin tuwo kadai aka yi ciki ba.
Kwatsam ran nan sai ga tsohon shugaba Jonathan a qasar Amurka, wata babban makarantar koyar da al’amuran dimokudadiyya ta qasar ta gayyace shi gabatar da wata qasida game da dorewar zaman lafiya bayan zabubbuka a nahiyar Afrika, kamar yadda hakan ya wanzu a qasashen Najeriya da Tanzaniya, inda wata qungiyar qasashen rainon Ingila, watau Kwamanwel ta tura shi don tabbatar da zaman lafiya bayan zaben shugaban qasa a can. A can Amurka ne fa ya ga zai iya mayar wa Obasanjo da martani, shi ma ya yi masa aibi ko illar da za ta rage masa qima a gaban iyayen gidansa, daidai da yadda shi ma ya yi masa a gaban ‘yan Najeriyar da ya mulka.
Ai fa ta inda Goodluck Jonathan ke shiga, ba ta nan ya dinga fita ba, wajen sukan lamirin Obasanjo, domin kuwa an ce ai a ranar fada ne ake gori, to Goodluck Jonathan ya kai fadansa da Obasanjo har qasar Amurka, inda ya yi masa tatas, ya nuna cewa shi santolabi ne da ya kasa shawo kan majalisar da ta fi qarfinsa don amincewa da baqin burinsa na zarcewa bisa karagar mulki a karo na uku. Goodluck Jonthan ya ci gaba da cewa a lokacin hakan da majalisar dokoki ta yi shi ne abin da ya fi dacewa, domin kuwa qasashen Afirka ba su buqatar shugabannin da za su zauna dirshan bisa mulki, ba ranar sauka, suna kuma bayar da cikakken goyon baya ga majalisun dokokin qasashen don su ji dadin yunqura wa don daqile baqin burin duk wani shugaban da ya yi gigin haka. A taqaice dai Jonathan ya nuna wa masu masaukinsa a Amurka cewa ra’ayin wasu shugabanni na yin gyara ga kundin tsari mulki don yin kwaskwarima ga tsawon wa’adi da kuma yawan lokutan da shugaba zai iya yin takara bai dace da tsarin qasashen da ke bisa tafarkin dimokuradiyya ba, kuma hakan ne ke raunana ginshiqan da ke tallabar dimokuradiyya.
To amma ai idan tsohon shugaba Jonathan ya samu rana a Amurka, har kuma ya yi shanya, ai wadanda ya yi wa lacca game da fa’idar dimokuradiyya da kuma yadda ta kasance a Najeriya sun san cewa ya fadi son ransa ne kawai, domin shi ma ya muzguna wa Cif Obasanjo. Idan Jonathan ya zargi Obasanjo da qoqarin miqe qafa bisa mulki a shekarar 2007, shi kuma fa, me ya nemi ya yi a lokacin da yake bisa tasa karagar? Shi da jam’iyyarsa ta PDP sun qyale dimokuradiyya ta yi tasiri a cikin harkokin gudanar da jam’iyyarsu? Sun qyale wasu su yi gogayya da shi a wajen fitar da dan takara? Ai babu wanda ya mance yadda shi ma Jonathan din ya yi ta kama-karya, yana tuttube shugabannin jam’iyya yadda ransa ke so, kamar yadda Cif Obasanjo ya dinga canja shugabannin Majalisar Dattijai kamar rigar “agbadar” da yake kwabewa a duk lokaci da ya nishadu.
Baicin haka nan kuma ta yaya Goodluck Jonathan zai iya kallon fuskokin Amurkawa, ya ce da su shugabannin Amurka ya yawan canja kundayen tsarin mulkin qasashensu don yin gyararraki ga dokokin wa’adin mulki, alhali kuwa shi ma ya gwada haka, don ya samu damar zarcewa a karo na uku, amma abin bai yiwu ba. Ai kowa ya san yadda haka nan, da rana tsaka, ya tsiri wani taron qasa a shekarar 2014 don a canja dokokin kundin tsarin mulki, ta yadda zai ji dadin zarcewa bisa mulki, ya kuma samu damar yin canje-canjen da za su ba shi ikon sake tsarin Najeriya yadda hakan zai ba ‘yan qabilarsa damar yi wa sauran ‘yan Najeriya hawan qawara, bayan sun samu sukunin dawwama bisa mulki sai baba-ta-gani.
Goodluck Jonathan dai ba shi da bakin magana game da wadancan abubuwan da ya zargi Obasanjo da aikatawa, walau a nan cikin gida ko a qasashen qetare, domin kuwa dukkansu danjuma ne da danjummai, tamkar kare da dila suke, babu wanda bai ciwon wani. Dukkansu sun nuna mana ra’ayi irin na ‘yan kudu, wanda ya tabbatar mana da cewa ba su naqalci dabarun mulki ba, babu kuma waninsu da nan gaba zai iya kamanta adalcin da ke zaunar da qasar nan lafiya irin yadda yanzu haka ke wanzuwa a qarqashin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Yanzu dai an yi yunwa, halin kowa ya fito, tsakanin ubangida da dangidansa, dukkan tsare-tsaren da suka yi don dawwama bisa mulki ta yadda za su ji dadin takura wa yankin Arewa sun bayyana, an kuma gane manufarsu. Saboda haka babu wani sabon abu game da abubuwan da Jonathan ya bayyana a qasar Amurka dangane da yunqurin Obasanjo na tabbata bisa mulki, domin kuwa kunkuru ne ke yi wa bushiya qafa.