Kunna talabijin

Wani Bafulatani ne ya je birni sai ya ga talabijin kuma ta burge shi. Domin ya burge ’yan uwansa a kauye sai ya saya ya biya kudi. Mai kanti ya ce masa: “Ai da ka je gida ka sa mata wuta sai kallo kawai!” Shi kuwa Bafulatani cikin sauri ya dauki akwatin talabijin, yana zuwa […]

Kunna talabijin
Kunna talabijin

Wani Bafulatani ne ya je birni sai ya ga talabijin kuma ta burge shi. Domin ya burge ’yan uwansa a kauye sai ya saya ya biya kudi. Mai kanti ya ce masa: “Ai da ka je gida ka sa mata wuta sai kallo kawai!” Shi kuwa Bafulatani cikin sauri ya dauki akwatin talabijin, yana zuwa gida sai ya tattara karmami da yayi, ya rufe talabijin, ya banka mata wuta. Ya koma gefe daya yana kallon ikon Allah.
Daga Nafisa Basiru Sadi, 07037902893