Kura da kallabin kitse
Wai yaya lafiyar kura balle ta yi hauka? A kwanakin baya, tun kafin a dage takunkumin yakin neman zabe, ‘ya’yan wata kungiyar goyon bayan Shugaba Goodleck Jonathan mai suna Transformation Ambassadors of Nigeria, TAN sun yi ta karaikana a fadin kasar nan suna fafutukar tallata shi da sunan janyo hankalinsa don ya amince, ya fito […]
Wai yaya lafiyar kura balle ta yi hauka? A kwanakin baya, tun kafin a dage takunkumin yakin neman zabe, ‘ya’yan wata kungiyar goyon bayan Shugaba Goodleck Jonathan mai suna Transformation Ambassadors of Nigeria, TAN sun yi ta karaikana a fadin kasar nan suna fafutukar tallata shi da sunan janyo hankalinsa don ya amince, ya fito don tsayawa takarar shugabancin kasa. Wannan jirwaye ne aka yi mai kama da wanka, domin kowa ya san cewa yakin neman zabe ne aka yi gadan-gadan domin kuwa abubuwan da suka wakana a wannan yunkurin ba su sha bamban ba da irin wadanda ake wanzarwa a lokutan yakin neman zabe ba. Abin da ya kara tabbatar da haka shi ne ganin yadda aka yi barin kudi na fitar hankali wajen tsare-tsaren bukukuwan da aka yi a dukkan manyan biranen jihohin kasar nan, kafatan dinsu.
Manya-manyan ministocin gwamnatin Jonathan, ‘yan asalin shiyyar Kudu-maso-Gabas da ‘yan kalilan daga Kudu-Kudu ne suka yi uwa, suka yi makarbiyar a wannan al’amari, su ne kuma suka yi kidarsu, suka yi rawarsu, su ne suka yi barin kudi, ‘yan uwansu ne kuma suka kwashe abinsu. Talakawan Najeriya sun cika da mamaki ganin yadda aka yi ta facaka da dukiyar da ba a san zafinta ba, da kuma yadda aka yi amfani da ita ta hanyoyin da ba su kamata ba don toshiya da rashawar da ta kara janyo wa jam’iyyar PDP da shugabanninta bakin jini da kyama, har ma a wasu wuraren aka yi ta kyarar masu goyon bayanta.
To ashe wancan abin da aka yi wasan yara ne bisa ga abin da ya wakana a ranar 20 ga watannan yayin da aka yi wani gagarumin taron cin abincin dare don yi wa Shugaba Goodluck Jonathan ajon makudan kudi don yakin neman zabensa, kuma makudan kudaden da aka tara cikin dan kankanen lokaci sun tayar da hankulan mutanen da ke tunanin abin da zai je da wanda zai zo, domin kuwa hakan ya nuna cewa shugabannin jam’iyyar PDP da kuma ‘ya’yanta da manyan abokai da makararraban Jonathan duk duwatsun cikin ruwa ne, ba su san ana rana ba. Sun nuna rashin kulawa ko rashin damuwa da halin da ‘yan uwansu ke ciki da kuma yanayin rayuwarsu cikin kunci da mayatar matsin da ke hana su more gardin rayuwa. Cikin kiftawa da bisimilla abokai da makararraban Jonathan suka ganganda tara masa Naira miliyan dubu uku cif-cif, kamar wadanda suka dauki tsinke, suka sakace hakorarsu, ba tare da nuna wata damuwa ba. Haka nan cikin ruwan sanyi hamshakan ‘yan kasuwa da fitattun ‘yan kwangilar da suka rufa, suka tayar da kai, hade da jiga-jigai da kusoshin jam’iyyar suka hada wasu Naira miliyan dubu goma sha takwas nan take, suka mika masa a matsayin tasu gudummawar.
Wannan al’amari ya daure wa jama’a da yawa kai har suna cewa da walakin, wai goro a miya, musamman ma ganin cewa ba domin Allah da Annabi ne aka tattara wadancan kudin ba, zubin adashi ne aka yi, kuma akwai ranar da za su kwasa, domin kuwa wanda duk ya ci ladar kuturu zai yi masa aski. To amma wadancan mutanen da suka zake wajen aikata riya muraran suna ina sa’ilin da jama’arsu suka kasance cikin wahalhalun da suka kasa magancewa saboda tsabar bakar fatarar da ta hana su katabus? Sai a yanzu ne za su nuna cewa suna da dukiyar gudummawar buki, amma ba su da zuciyar taimakon bayin Allah da suke tare da su dare da rana, ba su san cinsu ba, ba su kuma san cinsu ba?
Suna ina ‘ya’yan makwabtansu ke kangarewa domin iyayensu ba su iya biya masu kudin makaranta, suna zamewa ‘yan daba? Wace gudummawa suka bayar ga wadanda ke yawan bidar taimako a gidajen rediyo don tsira daga ukubar cutar da ta hana su daukar nauyin iyalanasu? Suna sane cewa matar dan uwansu ta arce, ta bar shi kwance ranga-ranga don ta gaji da jinyarsa sakamakon wata rikakkiyar kabar da aka rasa kudin yi masa aikin tiyata don raba shi da ita? Za su iya hakikancewa ba su san cewa yunwa na zauta wasu makwabtansu ba? Me suka yi don taimaka wa daruruwan dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita a jihohin Borno da Yobe da Adamawa don sake tsugunar da su ko hada su da iyalansu? Su ba wannan ne damuwarsu ba, alabarshi su je, su mutu ma ba su da sara. Su abin da ya fi damunsu, shi ne, yadda za su tsakuro kalilan daga dukiyarsu ta haram su taimaka wa wani azzalumi, don idan ya haye su kwashi kasiran. To Allah Ya sawwake, Ya kuma hana su kai wa ga biyan wannan mummunar bukatar.
Wadannan kudi tamkar kanwar bakI ce, amma sai dai da aka dibe ta ba a bai wa awakin baki ita ba. Sanin kowa ne wadancan jiga-jiga ‘ya’yan jam’ioyyar PDP, kuma na hannun daman Jonathan da ke sahun gaba a kungiyar TAN, watau Mrs Diezani Allison Maduekwe da kuma Mrs Stella Oduah ministoci ne da aka sha korafi akan su dangane da sama-da-fadi da aka ce sun yi da dukiyar talakawa, amma babu wani abin da aka yi don a tabbatar da gaskiyar haka, a kuma tatse dukiyar da suka hadidiya. Sai ga shi nan gaskiyar ta yi halinta, sa’ilin da suka mayar da wadancan kudin da aka kyautata zaton sun yi rub-da-ciki bisansu tamkar garin banza, domin kuwa sun yi farau-farau din banza da shi, sun ba wadanda ba su san ciwon kansu ba, sun sha a banza, sun kuma koma gefe guda, sun zura wa gwamnati ido don su karo. Abin takaici game da wannan mugun al’amarin shi ne ba kowa da kowa ne ke amfana ba daga waccan haramtacciyar garabasar ba, illa ya-nasu-ya-nasu, ko a hakan ma sai na kut-da-kut da su.
Wannan ne ya sa aka yi ta ganin wallensu, har ake kyamar su, kuma bisa ga dukkan alamu alhakin sauran jama’a da suka dauka ya zame dan kwikwiyon da ke biye da su, zai kuma gantsara musu cizo a lokacin da suke son cin gajiyarsa. Kudi dai ga ‘yan jam’iyyar PDP ba abin damuwa ba ne, ko nawa ake bukata su ganganda za su yi haka ba tare da wata damuwa ba, domin kowa ya san PDP kura ce da kallabin kitse. Amma abin tambaya shi ne kudin ajon da aka tarawa Jonathan za su wanke shi, ya fito fes a idanun talakawan Najeriya ganin cewa kazanta ne suka kara tara masa don ya ci gaba da bin kazantacciyar turba?