Kura-kuran da ya kamata a yi la’akari da su

Akwai kura-kurai da dama da mata suke yi wajen kwalliya ba tare da sanin hakan kuskure ba ne. Ya kamata a kiyaye idan an zo shafa kayan kwalliya a fuska; musamman wajen sanya gazal da hodar fandesho da jambaki da sauran kayan kwalliya wadanda ba su dace da launin fatar mutum ba. A yau na […]

Kura-kuran da ya kamata a yi la’akari da su

Akwai kura-kurai da dama da mata suke yi wajen kwalliya ba tare da sanin hakan kuskure ba ne. Ya kamata a kiyaye idan an zo shafa kayan kwalliya a fuska; musamman wajen sanya gazal da hodar fandesho da jambaki da sauran kayan kwalliya wadanda ba su dace da launin fatar mutum ba. A yau na lissafo kura-kuren da mata suke yi wajen kwalliya. In ko ba a gyara ba sai a ga mutum yana kama da dodo.

• Shafa hodar fandesho da ba ta dace da fatar mace ba: Sau da yawa sai a ga mace ta yi kwalliya da hodar fandesho da ba ta dace da launin fatarta ba. Ya kamata a samu launin fandesho da ya dace da launin fatar mace kafin a yi amfani da shi.

• Shafa kayan kwalliya a fuska mai gautsi:Idan aka shafa kayan kwalliya a fuska ba tare da shafa wa fuskar mai kadan ba lallai kwalliyan ba za ta yi kyau ba. Man jiki ko na fuska na gyara fata saboda haka, ya kamata ana shafa man fuska kafin shafa hoda.

• Idan kina da lebba manya bai kamata ki bi lebbanki da gazal ba. Domin yin hakan na kara fitar da girman lebbanki. Amma idan ke mai kananan lebba ne za ki iya bin lebbanki da gazal din baki (lip liner).

• Amfanin gazal a gira: Idan ke mai cikakkiyar gira ce, bai kamata ki dada gazal a kan girarki ba. Sai dai idan ke ba mai cikakkiyar gira ba ce za ki iya cika girarki da gazal wanda launi daidai yake da gashin girarki.

• Kwanciya da kwalliya a fuska:  Kwanciya da kwalliya ba karamin kuskure ba ne. Domin hakan na haifar da kurajen fata wadanda ke da wahalar magance su. Sinadaran kwalliya na illata fata a duk lokacin da aka kwanta barci da ita a fuska sai a kula.