Kura-kuren da mata ke yi wajen zaben miji
Kowace mace burinta ta samu miji nagari, wanda zai kula da hakkinta, ya rike mata amana, ya kuma kare mata mutunci. To amma mafi yawan mata sukan tafka kuskure yayin da samari suka nuna suna son su da aure, a karshe su yi biyu-babu, lamarin ya sukurkuce saboda halin da suka nuna tun farko.Wadansu matan […]
Kowace mace burinta ta samu miji nagari, wanda zai kula da hakkinta, ya rike mata amana, ya kuma kare mata mutunci. To amma mafi yawan mata sukan tafka kuskure yayin da samari suka nuna suna son su da aure, a karshe su yi biyu-babu, lamarin ya sukurkuce saboda halin da suka nuna tun farko.
Wadansu matan da zarar sun samu saurayi, maimakon su fada masa gaskiya sai dai karya. Tun daga farko idan ya tambaye su sunansu, sai su fada masa sunan karya.
Wata sai tafiya ta yi tafiya sannan ta fito ta fada masa sunanta na gaskiya, daga nan rashin yarda ya shiga tsakaninsu, saboda karyar da ta yi masa tun farko.
Wata kuwa sai ta kasa fada masa gaskiya, daga bisani idan ya gano sunanta na gaskiya sai ya guje mata ya nemi wata.
Wata budurwar ko bazawara maimakon ta fada wa saurayin gaskiyar yadda danginsu yake, sai ta rika nuna masa cewa su masu arziki ne, kuma iyayenta masu daukaka ne, daga bisani idan saurayin ya gane sai ya guje ta saboda karyar da ta yi masa.
Wadansu matan kan nuna wa saurayi karanta, idan suna so su yi magana da shi, sai su rika yi masa filashin, don ya kira su, ba za su taba kiransa a waya ba. Wannan halayyar kuskure ce, don takan sanya saurayi ya tsani budurwarsa, saboda mutane da yawa ba sa so a rika yi musu filashin.
Saurayi ko wanda zai kara aure ba ya so mace ta rika nuna kwadayinta a fili. Duk macen da ke nuna wa namiji kwadayi, to babu shakka ta yi kuskure.
Idan kina son wani abu sai ki tambaya ta hanyar ladabi da biyayya, sannan kada ki nuna masa kina son abu a fili har ya gane kin zaku. Mafi yawan mata da zarar sun ga wani abu sai su gallabi mutum har ta kai ya daina zuwa wurinsu.
daya daga cikin dabi’un da mai neman aure ba ya so shi ne, mace ta rika yi masa shisshigi da iya-yi. Muddin kina yi wa mai neman auren ki haka, babu shakka zai tsane ki. Mata da yawa ba su gane lokacin da ya kamata su shiga wani sha’anin mai neman aurensu da kuma lokacin da bai kamata ba. Galibi wasu matan sukan wuce gona da iri wajen danginsa da abokansa har ta kai an fara samun gutsuri-tsoma daga bisani rai ya baci.
Wani kuskure da mata ke yi shi ne, da yawansu ba sa nuna damuwa da irin son da ake yi musu. Duk abin da ya same shi, na murna ko na bakin ciki, ba za su nuna wata damuwa ba. Babu shakka wannan dabi’a tana sa mace ta fita daga ran namiji. Ya kamata a kiyaye.
boye so da kauna: Wannan dabi’a tana daga cikin manyan abubuwa da ke bata neman aure. Ya sanya a rika gudun mata, yakan kasance saurayi na so a rika fada masa ana son sa fiye da kowa kirikiri. Don shi ba zai iya fahimtar jirwaye mai kamar wanka ba. Shi kuwa wanda ya taba aure yakan fahimci inda mace ta sa gaba. Shi ba sai ta fito kiri-kiri ta gaya masa ba, amma shi ma idan ya lura ba a bayyana son ta hanyar da ta dace ba, to zai daina zuwa.
Kamata ya yi ’yan mata da zawarawa su fahimci iya mu’amala da ladabi da biyayya da gaskiya da rikon amana su ake bukata.
Za a iya tuntubar Abubakar a wannan lambar: 08027406827 ko kuma ta imail:[email protected]