kura ta lafa a Aba bayan harin IPOB ga ’yan Arewa
Ya zuwa rubuta rahoton nan, kura ta lafa, hankali ya kwanta a unguwar Hausawa da ke garin Aba, Jihar Abiya bayan farmakin da wadanda ake kyautata zaton ’yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biyafara ne suka kai musu a Talata da ta gabata. Kafin wannan hari na ranar Talata, sojoji da sauran jami’an tsaro […]
Ya zuwa rubuta rahoton nan, kura ta lafa, hankali ya kwanta a unguwar Hausawa da ke garin Aba, Jihar Abiya bayan farmakin da wadanda ake kyautata zaton ’yan kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biyafara ne suka kai musu a Talata da ta gabata.
Kafin wannan hari na ranar Talata, sojoji da sauran jami’an tsaro sun kai samame garin Umuahiya, mahaifar Kanu, shugaban kungiyar ta IPOB, da nufin sake kama shi, inda membobin kungiyar suka huce haushi kan al’ummar Arewa mazauna garin Aba, inda suke gudanar da harkokin kasuwancinsu da dadewa.
A shekara ta 2000, an taba kai wa ’yan Arewar wani kazamin hari a unguwar Hausawa da kuma kasuwar albasa, inda aka rasa rayuka. Harin da ya wakana sakamakon kafa shari’ar Musulunci da wasu gwamnatocin Arewa suka yi a jihohinsu.
A harin na makon nan, an rika bin ’yan Arewa da ke gudanar da kananan sana’o’i, aka rika raunata su da makamai. Da yake wa Aminiya karin bayanin yadda aka kai musu harin, Haladu Imam, dan kasuwa mazaunin Aba ya ce: “Kimanin sama da mutum 40 aka yi wa raunuka amma ba zan iya tantance adadin wadanda aka kashe ba.”
Ya ci gaba da cewa: “kura ta lafa a halin yanzu, domin an aiko mana da jami’an tsaro kuma gwamna ya kafa dokar-ta-baci ta tsawon kwana uku.”
Da yake yi wa Aminiya karin bayani dangane da wadanda aka kashe a lokacin farmakin, Alhaji Salisu danwanzan, shugaban kasuwar Albasa da ke Aba ya ce: “Mutum shida muka samu gawarwakinsu. Mun samu gawar mutum biyu a kasuwar doya, sai gawar wasu mutum biyu a kasuwar sabon layi, yayin da kasuwannin Oku Mango da Urata mutane daidai jimlar mutum shida ke nan, yanzu haka suna dakin adana gawa.” Ya tabbatar wa Aminiya cewa komai ya wuce, kura ta lafa. “Yanzu kam babu wata matsala, zancen nan da muke yi ma ina kasuwarmu ta albasa, an baza jami’an tsaro ko’ina babu wata fitina.”