kura ta lafa a Kalaba, bayan halaka dan Arewa

kura ta lafa a garin Kalaba, musamman unguwar Hausawa da ke layin Bagobiri, Jihar Kurosriba, sakamakon baza jita-jita da aka rika yi, cewa wai wani dan Arewa, mai sana’ar goge takalmi ya kashe wani dan asalin jihar a wata takaddama da ta hada su kan kudin aikinsa Naira 50. Lamarin da ya kai ga yi […]

kura ta lafa a Kalaba, bayan halaka dan Arewa
kura ta lafa a Kalaba, bayan halaka dan Arewa

kura ta lafa a garin Kalaba, musamman unguwar Hausawa da ke layin Bagobiri, Jihar Kurosriba, sakamakon baza jita-jita da aka rika yi, cewa wai wani dan Arewa, mai sana’ar goge takalmi ya kashe wani dan asalin jihar a wata takaddama da ta hada su kan kudin aikinsa Naira 50. Lamarin da ya kai ga yi wa wasu daga cikin ’yan Arewa masu kananan sana’o’i da suke yawo cikin gari, ana yi musu kwanton bauna ana lahanta su ko kwace masu kayan sana’a.
Wasu ’yan Arewa da aka zanta da su, sun nuna cewa ’yan kudancin kasar nan na yawan sanya su aikin wanke takalma kuma su hana masu hakki, su zage su, su ce masu Boko Haram ko kuma su rika ce masu nan ba Arewa ba ce, ba za a  biya ka ba, da sauran bakaken kalamai.
Ranar Lahadi 31 ga Janairun da ya gabata ce, a unguwar Afah Nsah, karamar Hukumar Kalaba ta Kudu, wani mai sana’ar wanke talakalma, mai suna Musa Ibrahim, kamar yadda Aminiya ta samu labara, husuma ce ta hada shi dan asalin Kurosriba da ya wanke masa takalmi, ya ba shi kudi domin ya nemo canji ya cire nasa ya ba shi canji. Bayan da shi Musa ya yawata bai samu canji ba sai ya dawo wa da mutumin kudinsa, shi kuma ya ce ba zai biya shi kudin wanke talakmin ba. Sai fada ya kaure tsakaninsu, shi ne ake zarge shi cewa ya yi amfani da wani abu cikin kayan sana’arsa, ya daba wa abokin cinikinsa. Daga nan ne fa aka ce mutanen dake wajen ’yan asalin Kurosriba suka fada masa da duka, suka ci karfinsa, ya fadi kasa. Daga nan nefa suka ja shi zuwa wani kango suka watsa masa man fetur suka kona shi.  Ana cikin haka ne sai aka ce wasu suka sanar wa jami’an tsaro, kafin daga bisani suka kawo dauki, suka kai shi asibiti, inda rai ya yi halinsa.
Bayan afkuwar lamarin, an rika baza jita jitar cewa Bahaushe ya kashe dan asalin Kurosriba. Bayan an sanar wa Sarkin Hausawa, Alhaji Salisu Abba Lawal abin da ya faru da al’ummarsa sai amma kasancewar bay a gari, sai ya umarci sakatarensa, Alhaji Sha’aban Abdullahi da ya bi diddigin lamarin.
A bayaninsa, Sakataren ya ce: “An sanya shi aiki ne, wajen karbar hakkinsa ne rikicin ya barke. Ka san sarkin yawa ya fi sarkin karfi, su kuma dama kadan suke jira dan Arewa ya yi masu laifi su far masa da duka. Shi kuma a kokarin karbar hakkinsa ne suka fada shi da duka, suka ci karfinsa suka ja shi zuwa wani kango suka zuba masa fetur suka kona.”
Da Aminiya ta tambaye shi kowane hali ake ciki yanzu, sai ya ce: “kura ta lafa, ’yan Arewa sun ci gaba da fita harkokin neman dari da kwabonsu da suka saba amma kuma jami’an tsaro sun dukufa wajen ganin sun zakulo wadanda suka kashe Musa Ibrahim, wanda tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.”