kura ta lafa a unguwar Ijora Badiya
Hankula sun kwanta, sannan mutane sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum bayan da ’yan gareji na bangaren Ijora da na bangaren Badiya suka ba hammata iska, inda mutum uku suka mutu wasu da dama suka jikkata kwanan baya, a Jihar Legas.Aminiya ta gano cewa wasu daga cikin wadanda aka fasa wa gidaje […]
Hankula sun kwanta, sannan mutane sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum bayan da ’yan gareji na bangaren Ijora da na bangaren Badiya suka ba hammata iska, inda mutum uku suka mutu wasu da dama suka jikkata kwanan baya, a Jihar Legas.
Aminiya ta gano cewa wasu daga cikin wadanda aka fasa wa gidaje da dakuna a lokacin fadan sun koma dakunansu, sannan masu sana’o’i daban-daban sun bude shagunansu.
Malam Musa ya ce, “Abubuwa sun koma daidai, kowa ya koma harkokinsa. Mutane da dama sun dawo gidajensu da dakunansu. Masu sana’o’i sun koma sana’o’insu. Komai ya koma kamar yadda yake a da”.
To sai dai Muhammad Baba, wanda ya yi asarar kudi da kayyaykinsa sakamakon fadan, ya bayyana cewa ba zai koma dakinsa ba. “Gaskiya ne komai ya lafa, mutane sun ci gaba da harkokinsu, amma ni gaskiya ban koma dakina ba, na tashi daga wurin na koma wani wurin. Dalilin shi ne wannan layi da aka yi fadan wuri ne da ba ya rabuwa da hargitsi da fadan ’yan gareji. Ba a yin cikakken wata ba a yi tashin hankali a wurin ba kuma yawanci Yarabawa ne suke yi a tsakaninsu, amma da sun tashi fadan sai ka ga suna auka wa mutanenmu, ba gaira ba dalili. Wani ma bai san hawa ba, bai san sauka ba, sai kawai a auka masa a kashe shi. Wani ma wucewa ya zo yi ta wurin, sai kawai su kashe shi. Ka san su ’yan garejin sun yi alwashin kone unguwarmu shi ya sa ni ba zan dawo wurin ba”.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da jami’an tsaro su kai samame wurin don kame wadanda suke tayar da zaune-tsaye.
To sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Legas ya ci tura domin mai magana da yawun rundunar ba ta amsa wayar da aka buga mata ba. Amma wata majiya da ke kusa da rundunar ’yan sandan ta tabbatar wa Aminiuya cewa an kame mutane da yawa wadanda ake zargin suna da hannu a tayar da rikicin, kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da su a gaban kuliya.